“Tinubu Ya Kammala Karatu a Jami’ar Chicago Harda Lambobin Girmamawa”: Omokri Ya Magantu

“Tinubu Ya Kammala Karatu a Jami’ar Chicago Harda Lambobin Girmamawa”: Omokri Ya Magantu

  • Reno Omokri ya wallafa sakamakon binciken da ya gudanar da kansa dangane da lamarin takardar makarantar shugaban kasa Bola Tinubu
  • Omokri ya bayyana cewa ya kamata mutane su daina yada labarin cewa Tinubu bai halarci jami'ar ta Amurka ba
  • A zahirin gaskiya, Omokri ya ce Tinubu na daya daga cikin manyan tsoffin daliban jami'ar jihar Chicago

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Chicago, USA - Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni cewa karya ne ace shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai halarci jami'ar jihar Chicago da ke kasar Amurka ba.

Da yake wallafa a shafinsa na Twitter, magoyin bayan jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) ya ce binciken da ya gudanar nasa na kansa ya nuna cewa da gaske shugaban kasa Tinubu ya halarci jami'ar ta Amurka, kuma yana daya daga cikin manyan tsoffin dalibansu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: A Karshe Tinubu Ya Magantu Kan Dakatar Da Emefiele, Ya Ba Da Hujja Mai Karfi

Reno Omokri da shugaban kasa Bola Tinubu
“Tinubu Ya Kammala Karatu a Jami’ar Chicago Harda Karramawa”: Omokri Ya Magantu Hoto: Reno Omokri, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

"Karya ne ace Bola Tinubu bai halarci jami'ar jihar Chicago ba": Omokri ya magantu

Omokri, wanda ya kasance magoyin bayan babbar jam'iyyar adawa wanda ke bayyana ra'ayinsa a soshiyal midiya, ya yi kira da a yi taka-tsan-tsan wajen adawa da shugaban kasa Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Omokri ya rubuta:

"Bana neman kowani mukamin siyasa, ko aiki daga wajen Tinubu. Sai dai, karya ne ace Bola Tinubu bai halarci jami'ar jihar Chicago ba.
"Na je wajen da kaina. Na yi bidiyo daga sansaninsu. Na gana da jami'ansu.
"Tinubu ya halarta kuma ya kammala jami'ar jihar Chicago da lambobin girmamawa, sannan suna ma da hotonsa a cikin ofishin tsoffin dalibansu a matsayin daya daga cikin manyan tsoffin dalibansu.
"Ba wai zuwa wajen kawai nayi don falla Tinubu ba (don kawai na gano ko ya halarci makarantar), na kuma bukaci rijistran su ya rubuta abun da suka fada mani. Ga wasikar da suka bani a kasa.

Kara karanta wannan

“Tinubu Ya Nuna Kansa a Matsayin Mace Yayin Neman Gurbin Karatu a Jami’ar Chicago,” Shaidan Atiku Ga Kotu

"Kuma kuna iya ziyartan wajen da kanku kamar yadda na yi ko ku aika sakon yanar gizo ko ku kira su idan kuna shakkar wannan wasika da aka bani."

Yayin da yake bayyana cewa Tinubu ba waliyi bane, Omkori ya bukaci masu adawa da su yi adalci da gaskiya yayin adawa da shi.

Tinubu ya nemi gurbin karatu a jami'ar Chicago a matsayin mace, shaida

A wani labarin, mun ji a baya cewa shaida mai wakiltan jam'iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar ya yi wani fallasa mai ban mamaki a kotun zabe a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.

Shaidan Atiku ya sanar da kotun zaben shugaban kasar da ke zama a Abuja cewa takardar neman gurbin karatu a jami'ar Chicago da kwalejin South West ta yi da sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana shi a matsayin mace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng