"Wahala": Magidanci Ya Garzaya Kotu Neman a Raba Aurensa Da Matarsa, Kotu Tace Ba Aure a Tsakaninsu

"Wahala": Magidanci Ya Garzaya Kotu Neman a Raba Aurensa Da Matarsa, Kotu Tace Ba Aure a Tsakaninsu

  • Kotu ta gayawa wani magidanci mai neman a raba aurensa da matarsa cewa babu aure a tsakaninsu a shari'ance
  • Yana zarginta da faɗan tsiya da cin amanarsa yayin da matar ta zarge shi da rashin sauke nauyin da ke a wuyansa
  • Kotun ta ba matar kula da ƴaƴansu yayinda da umarci mijin da ya riƙa biyan kuɗin kulawa da su

Kotu ta gayawa wani magidanci mai son datse igiyar aurensa da matarsa na shekara 22 cewa babu aure a tsakaninsu a shari'ance.

Abayomi Oreyemi ya buƙaci kotun kostomare da ke a Mapo cikin birnin Ibadan da ta datse igiyar aurensa da Basirat Oreyemi, inda ya zargeta da faɗan tsiya da cin amanarsa, cewar rahoton Daily Nigerian.

Magidanci ya nemi kotu ta datse igiyar aurensa da matarsa
Kotun tace babu aure a tsakaninsu Hoto: Gettysburg images
Asali: Getty Images

Matar na da wani saurayi daban

Ya bayyana cewa matarsa tana da wani saurayi mai suna Baba Aliya, wanda yake yawan dawo da ita gida sannan ya lakaɗa masa duka idan ya yi musu magana.

Kara karanta wannan

"Zai Biya N10m Shigar Ciniki": Attajiri Dan Najeriya Na Neman Wacce Za Ta Haifar Masa Yaro, Zai Biya N20m

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa matarsa ta sanya ƴan sanda sun cafke shi ba tare da wani dalili ba sannan bata ganin mutuncinsa da na iyayensa.

Sai dai, Basirat Oreyemi, ta musanta zarge-zargen da yake yi mata inda tace mijin nata shi ne wanda baya sauke nauyin da ke wuyansa da cin zarafinta.

Bai biya kuɗin sadaki ba

Ta bayyana cewa bai biya kuɗin sadakinta ba, bai halarci jana'izar iyayenta ba, bai taimaka mata ba lokacin haihuwa sannan ba ruwan shi da karatun ƴaƴansu.

Ta kuma bayyana cewa ya ɓalle mata kofar ɗaki da ƙarfin ya shiga lokacin da bata nan inda har ya lalata ƙofar. Ta nunawa kotun shaidar ƙofar da ya lalata.

Shugabar kotun, Mrs S.M. Akintayo, ta yi hukuncin cewa babu auren da za a raba a tsakaninsu, saboda basu cika sharuɗɗan aure ba.

Kara karanta wannan

"Ta Hanyar Kyakkyawar Niyya": Matashiyar Budurwa Ta Fice Daga Makaranta, Ta Samu N2.1bn a Cikin Wata Shida

Ta bayyana cewa kafin aure ya halatta dole sai an biya sadaki, kawo amarya da bayar da kyaututtuka, wanda a cewarta ba su yi ko ɗaya ba daga ciki.

Ta bar yaran su ci gaba da kasancewa a ƙarkashin kulawar Basirat Oreyemi sannan ta umarci Abayomi Oreyemi da ya riƙa biyan N25,000 duk wata domin kulawa da su. Ta kuma hana shi tsangama, hantara ko katsalandan a cikin rayuwar Basirat.

Magidanci Ya Maka Surikansa Kara Gaban Kotu

A wani labarin kuma, wani magidanci ya kai ƙarar iyayen matarsa ƙara a gaban kotun shari'ar musulunci da ke a Kano, kan zargin ɓoye masa mata.

Magidancin yana ƙarar surikansa ne bisa laifin ɗauke masa matarsa ta Sunnah daga gidansa ba tare da izninsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng