Tinubu: Babu Cire Tallafin Mai a Jawabin Ranar Rantsuwa Amma Na Sanar da Cire Wa
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce waɗanda suka shirya masa jawabin ranar bikin rantsuwar kama aiki ba su sanya batun cire tallafin mai ba
- Shugaban kasan ya ce sai bayan ya hau mumbarin magana ya ji cewa ya kamata ya cire tallafin tun a ranarsa da farko a Ofis
- Tinubu ya ayyana tallafin a matsayin damfara da kuma taimaka wa 'yan fasa kwauri da wasu ƙasashen waje
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya ta jima tana biya a matsayin 'Damfara' kuma mai daƙushe ci gaban ƙasa.
Channels tv ta rahoto shugaban ƙasar na cewa tallafin na ƙara tallafawa yan fasa kwauri da kuma rage wa wasu ƙasahen Afirka wahalhalu da tashin farashi.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da mutanen Najeriya da ke rayuwa a ƙasar Faransa da wasu ƙasashe a nahiyar Turai.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Dele Alake, shi ne ya bayyana kalaman da Tinubu ya faɗa a wata sanarwa da ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda na cire tallafin mai duk da ba ya cikin jawabina - Tinubu
Shugaba Tinubu ya yi bayanin cewa masu ba shi shawara ta musamman, Wale Edun, da Dele Alake, ba su sanya batun cire tallafin man fetur ba a jawabinsa na ranar rantsuwar kama aiki.
A ruwayar Leadership, Bola Tinubu ya ce:
"Amma sai na ji a raina ya kamata na cire tallafin nan tun a rana ta farko da shiga Ofis. Da na hau kan munbari na ƙara samun kwarin guiwa, na ce tallafin mai ya tafi."
Wannan ne karo na farko da shugaba Tinubu ya yi tsokaci kan jawabinsa na ranar rantsuwar kama aiki, ranar 29 ga watan Mayu, 2023, lokacin da ya sanar da cewa tallafin mai ya tafi.
Batun Nadin Ministoci: Fitacciyar Lauya Ta Shawarci Tinubu Ya Gujewa Jiga-Jigan Kurakurai 5 Da Buhari Ya Yi
Kalaman ya haddasa tashin farashin litar mai nan take da kuma ƙarancinsa a faɗin ƙasa, lamarin da ya jawo ƙungiyar kwadugo ta fara kiran a fara zanga-zanga.
Muna Kan Aikin Kawo Hanyoyin Rage Radadin Cire Tallafin Mai A Najeriya, Tinubu
A wani labarin na daban kuma Shugaban kasa ya ce gwamnatinsa na shirin kawo hanyoyin rage wa 'yan Najeriya radaɗin cire tallafin mai.
Tinubu ya tabbatar da cewa tuni aka gama aikin lalubo hanyoyon rage wa 'yan Najeriya raɗaɗi da ƙuncin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng