“Tsarin Kudin Kasar Ya Lalace a Karkashin Emefiele” Inji Shugaban Kasa Tinubu
- Daga karshe shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana dalilinsa na kama gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- A wata ganawa da ya yi da yan Najeriya mazauna waje a kasar Faransa a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, Tinubu ya ce harkokin babban bankin kasar karkashin Emefiele ya lalace
- Sai dai kuma Tinubu ya bayyana cewa Emefiele na hannun hukumomin inda ya ce za a kammala shari'arsa nan ba da jimawa ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, ya bayyana sabon matsaya dangane da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Tinubu ya yi magana a yayin tattaunawa da yan Najeriya mazauna kasar Faransa da kasashen da Turai da ke makwabtaka a gefen taron Duniya a babban birnin kasar Faransa, Paris.
CBN karkashin Emefiele, Tinubu ya magantu
Shugaban kasar ya ce tsarin kudin kasar a karkashin dakataccen gwamnan na CBN ya lalace, jaridar The Nation ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu ya magantu kan dakatar da Emefiele, ya bayyana abun da ya kai ga shigarsa halin da yake ciki
Ya ce yan Najeriya da dama mazauna waje sun gaza tura kudi ga yan uwansu saboda farashin chanjin kudi, cewa wannan ya zama tarihi a yanzu.
Da yake magana kan lamarin dakataccen gwamnan na CBN, Tinubu ya ce:
"Lokacin tsarin kudi ya lalace. Yan mutane kadan ke kunshe kudadenmu a jakunkuna sannan kuma ku da kanku, kun daina tura kudi gida ga iyayenmu talakawa. Kafofi da dama...amma wannan ya zama tarihi a yanzu, ya zama tarihi.
"Mutumin na a hannun hukumomi, ana yin wani abu a kai, za su sasanta kansu."
An shawarci Tinubu kan wanda zai nada a matsayin sabon gwamnan CBN bayan dakatar da Emefiele
A wani labari na daban, mun ji cewa an shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da al'adar nan na nada ma'aikatan banki a matsayin gwamnonin babban bankin Najeriya (CBN), dadaddiyar al'adar babban bankin kasar.
Deji Adeyanju, wanda ya kasance dan fafutuka na Najeriya shine ya bayar da shawarar a wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng