Dakarun Sojin Najeriya Sun Sheke 'Yan Ta'addan ISWAP Guda 6 a Jihar Borno
- Gwarazan sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe yan ta'addan kungiyar ISWAP guda 6 a yankin ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno
- Zagazola Makama ya bayyana cewa yan ta'addan da sojin suka kashe suna da haɗari, su ke dasa bama-bamai a kan hanyoyi
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya kai ziyarar jaje da wasu ƙauyuka da yan Boko Haram suka kashe mutane
Borno - Dakarun sojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas sun sheke mayaƙan kungiyar 'yan ta'addan ISWAP 6 a Banki, jihar Borno
'Yan ta'addan sun gamu da ajalinsu ne a hannun dakarun soji ta musamman tare da haɗin guiwar jami'an Civilian Joint Task Force (CJTF) ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni, 2023.
Sojojin sun yi wa 'yan ta'addan kwantan ɓauna kana suka samu nasarar aika su lahira a yankin Bula Yobe kuma a titin Darajamal a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa 'yan ta'addan da sojojin suka hallaka suna da matuƙar hatsari domin su ke dasa bama-bamai a kan hanyoyi su yi wa jami'an soji kwantan ɓauna.
Mayakan Boko Haram sun kashe matasa 8
Haka nan kuma mayakan Boko Haram sun halaka matasa 8 a yankin kananan hukumomin Mafa da Jere duk a jihar Borno.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa hudu daga cikin matasan sun fita nemi itacen ƙonawa a Tamsu-Ngamdu lokacin da suka ci karo da 'yan ta'addan.
Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya kai ziyarar ta'aziyya zuwa garuwawan da lamarin ya shafa ɗaya bayan ɗaya ranar Jumu'a.
Zulum ya tabbatar musu da cewa gwamnati ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen kawo karshen matsalar tsaro a faɗin jihar Borno.
Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kaduna, Sun Kashe Mutane Sun Sace Matafiya
A wani labarin na daban 'Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari kauyen Sabon Layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'addan sun kashe manoma 3, sun tattara wasu da matafiyan da suka nufi kasuwar mako, sun yi awon gaba da su.
Asali: Legit.ng