Zulum Ya Yi Allah Wadai Da Ta'asar Da 'Yan ISWAP Suka Yi A Borno, Ya Ce Alwashin Daukan Mataki
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana takaicinsa dangane da kisan manoma takwas da 'yan ta'addan ISWAP suka yi
- Maharan, waɗanda suka zo a kan babura ɗauke da manyan bindigu, sun farmaki wasu garuruwa shida a jihar ta Borno
- Gwamnan ya sha alwashin samar da wata ƙungiya ta tsaro ta musamman, domin bayar da kariya ga manoma a jihar
Maiduguri, Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayyana alhininsa dangane da kisan wasu manoma takwas da mayaƙan Daular Islama Ta Yammacin Afrika (ISWAP), suka yi a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, kisan ya afku ne a garuruwan Shuwarin, Tomsu Ngamdu, Baram Karauwa da Muna a ranar Alhamis, da misalin karfe 1:00 na rana a yayin da manoman ke aiki a gonakinsu.
Zulum wanda ya ziyarci Mafa, ya bayyana harin a matsayin abin takaici, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.
Zulum zai dauki ƙwaƙƙwaran mataki dangane da harin
Ya ce gwamnatin jihar za ta haɗa gwiwa da jami’an tsaro domin tura karin sojoji don tabbatar da tsaron gonakan da manoman ke nomawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Zulum:
“Gwamnatin jihar za ta kira taron majalisar tsaro na gaggawa domin samar da hanyoyin tabbatar da isasshen tsaro ga manoma.”
“Gwamnati za ta kuma ƙaddamar da tawagar 'Agro Rangers', da za ta ƙunshi jami’an tsaro na Civil Defence, Sojoji, 'yan ƙato da gora, da kuma mafarauta domin kare manoman.”
Gwamnan ya ce matsalar ƙarancin abinci ita ce mafi muni fiye da rikicin Boko Haram, inda ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don ganin jama’a sun samu damar noma gonakinsu.
Maharan sun zo a kan babura ɗauke da AK47
Tun da farko wani da ya shaida faruwar lamarin mai suna Yarima Goni, ya shaidawa Zulum cewa ‘yan ta’addan na ISWAP sun zo ne akan babura ɗauke da bindiga ƙirar Ak47.
Wani da shima ya shaida faruwar lamarin, Malam Bukar Grema, ya shaida wa gwamnan cewa an binne mutane uku da harin ya rutsa da su a Shuwarin.
Ya bayyana cewa yawancin waɗanda aka kashe, an ɗaure hannayensu ta bayansu.
A cewarsa:
"Mun gano gawarwakinsu da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Juma'a kuma anyi musu sallah da misalin ƙarfe 10:00 na safe."
Shereef Goni, wani da shima ya shaida lamarin, ya ce an samu ƙarin wasu mutane biyar da aka kashe a Tomsu Ngamdu.
Shareef ya ƙara da cewa ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da wasu mutane goma a yayin harin.
Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da maharan ke farmakar manoma a jihar Borno, domin ko a kwanakin baya, sai da maharan suka kashe manoma sama da 40 a ƙaramar hukumar Kala-Balge da ke jihar.
Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Mayar Da Muhuyi Magaji Kan Muƙaminsa Na Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa
Yan Boko Haram sun yi wa mutane 15 yankan rago a Borno
A wani labari makamancin wannan da Legit.ng ta kawo muku a makon da ya gabata, wasu mahara da ake tunanin 'yan Boko Haram ne, sun halaka mutane 15 ta hanyar yi musu yankan rago a jihar Borno.
An bayyana cewa maharan sun farmaki garuruwan da abin ya shafa guda biyu cikin tsakiyar dare.
Asali: Legit.ng