Bikin Sallah: Gwamna Aliyu Ahmed Ya Ba Da Umarnin Biyan Ma'aikatan Sokoto Albashinsu Cikin Gaggawa

Bikin Sallah: Gwamna Aliyu Ahmed Ya Ba Da Umarnin Biyan Ma'aikatan Sokoto Albashinsu Cikin Gaggawa

  • Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ba da umarnin a biya ɗaukacin ma'aikatan jihar da 'yan fansho albashinsu na watan Yuni cikin gaggawa
  • Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar hakan ne don bai wa ma'aikatan jihar da 'yan fansho damar gudanar da bikin sallah cikin walwala
  • Sanarwar biyan albashin da kuɗaɗen 'yan fanshon ta fito ne ta hannun sakataren yaɗa labaran gwamnatin jihar, Abubakar Bawa a ranar Alhamis

Sokoto - Gwamnan Ahmed Aliyu na jihar Sokoto, ya bayar da umarnin a yi gaggawar biyan kafatanin ma'aikatan jihar kuɗaɗensu na albashin watan Yuni da muke ciki.

Haka nan gwamnan ya kuma ba da umarnin a haɗa da ɗaukacin 'yan fanshon jihar cikin waɗanda za a biya kuɗaɗen, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Dakatar da Ciyamomin Kananan Hukumomi 23, PDP Ta Maida Martani Mai Zafi

Gwamnan Sokoto ya ba da umarnin biyan ma'aikata albashinsu
Gwamnan Sokoto ya ce a biya ma'aikatan jihar albashinsu kafin sallah. Hoto: Ahmed Aliyu TV
Asali: Facebook

Za a biya albashin don bai wa ma'aikata damar yin bikin sallah cikin walwala

Gwamna Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, ta hannun sakataren yaɗa labaransa, Abubakar Bawa, cikin wata takarda da ya sanyawa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yi hakan ne domin bai wa ma'aikata da 'yan fanshon jihar, damar gudanar da shagulgulan bukukuwan Sallah mai zuwa cikin walwala da jin daɗi.

Gwamna Aliyu Ahmed ya roki ma'aikatan Sokoto da su kiyaye haƙƙoƙin aikinsu

Gwamna Aliyu ya kuma tabbatarwa ma’aikatan jihar ta Sokoto, aniyar gwamnatinsa na ganin ta farfaɗo da martabar ma’aikatan ta hanyar tabbatar da jin daɗi da walwalarsu a kowane lokaci.

Bayan haka ne kuma gwamnan ya yi kira ga ma’aikatan jihar da su yi ƙoƙarin nuna godiyarsu ta hanyar kiyaye lokaci, gami da gaskiya da sadaukarwa a wajen aikinsu, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan PDP a Arewa Zai Fara Ciyo Bashin N15bn Ƙasa da Wata 1 Da Hawa Mulki

Sannan ya kuma yi kira ga ɗaukacin al’ummar jihar, da su ci gaba da yi wa gwamnatinsa addu’a, wajen ganin ta samu nasarar biyan bukatunsu da ta yi alƙawari.

Gwamnan Sokoto ya kori sakatarorin jihar 23

A wani rahoto da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya sanar da korar ilahirin sakatarorin ilmi na duka ƙananun hukumomi 23 da ke jihar.

Gwamnan ya kuma umarci korarrun sakatarorin ilimin da su miƙa ragamar gudanarwarsu ga mafiya ƙololuwar muƙami a ofisoshin nasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng