Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kaduna, Sun Kashe Mutane Sun Sace Matafiya
- 'Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari kauyen Sabon Layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna
- Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'addan sun kashe manoma 3, sun tattara wasu da matafiyan da suka nufi kasuwar mako, sun yi awon gaba da su
- Kakakin rundunar 'yan sanda reshen jihar Kaduna ya ce rahoton harin bai iso ofishinsa ba amma zai nemi bayani daga yankin
Kaduna - Miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki yankin Sabon layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, sun halaka manona uku.
Rahoton jaridar The Nation ya tattaro cewa yan bindigan sun kuma tattara wasu manoma da matafiya sun yi awon gaba da su zuwa cikin dazuka.
Wani shugaban al'umma a yankin, Sallau Ibrahim, ya ce maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar rana yau Alhamis, 22 ga watan Yuni.
"Sun kashe manoma uku, Anas Sabonlayi, Abubakar Dankibiya, da kuma Harisu Unguwar Lemu," inji shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, yana hasashen wannan harin ɗaukar fansa ce kan lugudun wutan da rundunar soji ke ci gaba da yi a yankunan da 'yan bindigan ke samun mafaka.
Yan bindigan sun tare matafiya a hanyar zuwa kasuwa
Haka nan bayanai sun nuna yan ta'addan sun farmaki matafiyan da suka fito daga yammaci zuwa kasuwar Birnin Gwari da nufin cin kasuwar mako-mako ta ranar Alhmis.
A rahoton Leadership, Sallau ya ƙara da cewa
"Sun sace 'yan kasuwa da matafiya da ke kan hanyar zuwa kasuwa. Mako biyu kenan manoma ba su da sukunin zuwa gonakinsu, yau sun kama hanya ga shi an farmake su."
Rahoto ya nuna cewa tuni aka yi wa mamatan jana'iza a Sabon Layi da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Alhamis kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Da aka tuntuɓi shugaban ƙungiyar raya yankin Birnin Gwari (BEPU), Usman Kasai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce:
"Sun kashe mutun uku kuma sun sace mutane da yawa, a yanzu muna ta kokarin tantance adadin yawan mutanen da suka yi garkuwa da su."
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Haka nan da ake nemi jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce har yanzun bai samu rahoto ba.
Yan Bindiga Sun Sheka Barzahu Yayin da Suka Kai Wa Jami'an Tsaro Hari
A wani rahoton na daban kuma Yan banga sun sheƙe yan ta'adda uku yayin da suka yi yunkurin kai muau farmaki a jihar Anambra.
Rahoto ya nuna cewa 'yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan bangan da tunanin suna bacci da safiyar Litinin, 19 ga watan Yuni amma reshe ya juye da mujiya.
Asali: Legit.ng