NAFDAC: Taliyar Indomie Ta Najeriya Ba Ta Dauke Da Sinadarin Ethylene Oxide Da Nau'insa Masu Illa

NAFDAC: Taliyar Indomie Ta Najeriya Ba Ta Dauke Da Sinadarin Ethylene Oxide Da Nau'insa Masu Illa

  • Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa (NAFDAC), ta ce bincikenta a kan taliyar Indomie ya kammala
  • NAFDAC dai ta ƙaddamar da bincike ne a kan taliyar ta Indomie, biyo bayan wani sinadari mai suna ethylene oxide da aka ce ta na ɗauke da shi
  • Masana sun bayyana cewa, sinadaran na ethylene oxide, na sabbaba cututtuka masu wuyar sha'ani irinsu sankara a jikin ɗan adam

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa (NAFDAC), ta bayyana sakamakon binciken da ta gudanar a kan taliyar Indomie.

Darakta janar ta hukumar, Farfesa Christianah Adeyeye ce ta bayyana haka ranar Alhamis a Legas, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

NAFDAC ta kammala bincike kan Indomie da ake yi a Najeriya
NAFDAC ta ce Indomin da ake yi a Najeriya ba ta dauke da sinadarai masu matsala. Hoto: The Punch
Asali: UGC

NAFDAC ta gudanar da bincike a kan Indomie

Hukumar ta bincika indomin domin ganin ko ta na ɗauke da sinadarin Ethylene Oxide ko nau'o'insa, wanda sinadari ne mai matuƙar haɗari ga lafiyar ɗan Adam.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shettima Ya Sa Labule da Bill Gates, Ɗangote da Wasu Gwamnoni a Villa, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A binciken da aka gudanar, an gano cewa taliyar indomin wacce ake yi a Najeriya, da kuma kayan yajinta basa ɗauke da waɗannan sinadarai masu cutarwa.

Binciken na NAFDAC, ya samo asali ne daga bincike kan taliyar ta ‘Special Chicken Flavour’ da ma’aikatun lafiyar ƙasashen Malaysia da Taiwan suka yi kan zargin kasancewar sinadarin ethylene oxide a ciki.

Ethylene Oxide, wani sinadari ne da ke da alaƙa da kamuwa da cutar kansa.

Babu Indomie mai ɗauki da sinadarin ethylene oxide a Najeriya

Adeyeye ta ƙara da cewa an karɓi samfurin taliyar ta 'Chiken Flavour' da ma sauran nau'o'in taliyar da ake yi a kamfanonin Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

An yi hakan ne a cewarta domin tabbatar da an gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike kan duka nau'o'in taliyar da ake sanarwa a ƙasar, ba wai iya wacce ake maganar a kanta ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Mayar Da Muhuyi Magaji Kan Muƙaminsa Na Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

Ta kuma ƙara da cewa sun baza jami'an hukumar su a kasuwanni daban-daban da ke faɗin ƙasar nan da suka haɗa da Legas, Abuja da Kano, a yayin nemo samfurin.

A cewarta ma'aikatunsu sun yi hakan ne don tabbatar da cewa babu nau'o'in taliyar Malaysia da Taiwan ɗin a kasuwannin Najeriya.

Jaridar The Punch ta ce NAFDAC ta gudanar da binciken na ta ne a wani ɗakin gwaje-gwaje na hukumar a Oshodi da ke birnin Legas.

Daraktar ta kuma bayyana cewa baya ga ethylene oxide, hukumar ta bincika ƙarin wasu sinadaran da aka tabbatar suna da illa ga jikin ɗan adam, inda sakamakon ya nuna cewa babu su a cikin nau'o'in taliyar da ake amfani da ita a Najeriya.

NAFDAC ta hana shigowa da taliyar Indomie Najeriya

Legit a kwanakin baya ta kawo muku wani rahoto na cewa Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa (NAFDAC), ta dakatar da shigowa da taliyar Indomie Najeriya har sai ta kammala bincike.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

Hukumar ta yi zargin cewa akwai wani sinadari mai haɗari da ke haddasa cutar sankara a cikin Indomin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng