“Na Yi Nawa”: Matashi Ya Nemo Madadin Man Fetur, Ya Kunna Janareto Da Gas a Bidiyo
- Yayin da farashin man fetur ya yi tashin gauron zabi, wani bidiyon TikTok ya nuna wani janareto da ke aiki da iskar gas
- Bidiyon ya ja hankali mutane da dama da suka nuna sha'awarsu yayin da yan Najeriya da dama ke neman madadin man fetur
- Wasu mutane sun bayyana cewa tuni suka mayar da janaretonsu zuwa mai amfani da iskar gas, cewa yana aiki sosai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yayin da farshin man fetur ya yi tashin gauron zabi, wasu yan Najeriya suna neman hanyoyin da za su dunga tayar da janaretonsu.
Wani bidiyo da Orilomo ya wallafa a TikTok ya nuna wani janareto yana aiki da tukunyar gas ba tare da tangarda ba.
A halin yanzu, ana siyar da man fetur fiye da N500 kan kowace lita a biranen Najeriya da dama bayan gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur.
Iskar gas na aiki sosai a janaroto, inji masana
Sakamakon tsadar farashin man fetur, wasu masana harkar wuta sun fara wallafa bidiyoyi da ke nuna janareton mutane da suka mayar da shi zuwa mai aiki da iskar gas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bidiyon TikTok din, Orilomo ya nuna daya daga cikin janaroto da aka riga aka mayar da shi zuwa mai amfani da gas.
Legit.ng ta tuntubi Orilomo don jin dan takaitaccen bayani kuma ya ce janareton na aiki da kyau.
"Iskar gas din na aiki sosai. Za a iya amfani da 3kg na gas zuwa tsawon awanni 12. Yana aiki da kyau."
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Wasu mutane da suka kalli bidiyon Orilomo sun garzaya sashin sharhi domin tofa albarkacin bakunansu. Wasunsu sun bayyana cewa sun sauya nasu kuma yanzu da gas suke amfani wajen ta da janaretonsu.
Wasu kuma sun nuna damu dangane da hatsarin abun. Amma Orilomo ya bayar da shawarar cewa ya kamata wadanda za su yi amfani da janareton sun bayar da dan tazara a tsakanin janareton da tukunyar gas din.
@CROSS CITY CONSULT ya ce:
"Na zata ba zai yi kara ba faaaa."
@grace empire ta ce:
"Yana aiki da kyau. Na yi nawa."
@Shafson Almaskawee ya ce:
"Ya kamata janareton ya dan yi nesa da tukunyar gas din."
@2cleanautos ya ce:
"Ya za a yi ka daura gas din a saman janareto? Wannan na da matukar hatsari. Ka duba tsaron lafiya tukuna."
Tsadar man fetur: Gwamnan Neja zai samar da motar kyauta da zai dunga jigilar dalibai
A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Neja tana shirin samar da motocin kyauta don jigilar dalibai a makarantun gwamnatin jihar.
Gwamnatin na shirin daukar wannan mataki ne saboda tsadar abun hawa sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Asali: Legit.ng