Kashim Shettima Ya Sa Labule da Bill Gates, Gangote da Wasu Gwamnoni a Villa
- Kashim Shettima ya shiga ganawa yanzu haka da shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, Bill Gates, da Aliko Ɗangote a Villa
- Mambobin ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) na cikin waɗanda suka halarci taron wanda aka fara tun karfe 11:43 na safe
- Bill Gates ya kawo ziyara ƙasashen Najeriya da Jamhuriyar Nihar ne domin tattauna batun da suka shafi harkar lafiya da ci gaban kasa
FCT Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, na ganawa yanzu haka da shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, Bill Gates, da shugaban kamfanin Ɗangote, Aliko Ɗangote, a Aso Rock.
Rahoton Punch ya kawo cewa mambobin ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) na cikin wannan ganawa wacce ke gudana yanzu haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron, wanda aka fara da misalin karfe 11:43 na safiyar Alhamis, 22 ga watan Yuni, na cikin ɓangaren ayyukan da ziyarar Bill Gates a Najeriya da Jamhuriyar Nijar ta ƙunsa.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ganawa da Shettima ta zo awanni 72 bayan Mista Gates da Alhaji Ɗangote sun gana da shugaban kasa, Bola Tinubu, ranar Litinin a Villa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Me za'a tattauna a taron yau da Shettima?
Sai dai har kawo yanzun ba'a bayyana muhimman ajendojin da za'a tattauna a wannan ganawa ta ranar Alhamis ba, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Amma ana tsammanin mahalarta taron zasu maida hankali wajen yauƙaƙa dangantaka tsakanin gidaauniyar da Bill Gates ke jagoranta, gidauniyar Ɗangote da kuma gwamnatin Najeriya.
Haka zalika ana ganin taron zai fi maida hankali kan inganta alaƙar ɓangarorin uku musamman a ɓangaren lafiya kuma ilimi.
Mista Gates ya kawo ziyara Najeriya ne domin tattaunawa da shugabannin ƙasar da kuma abokan hulɗa da nufin lalubo hanyoyin magance kalubalen da suka turmushe harkar lafiya da ci gaba.
Jiga-jigan da suka halarci ganawar yau Alhamis a Villa
Gwamnonin da suka samu ikon halartar wannan taro sun haɗa da shugaban NGF kuma gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, Bala Muhammed na Bauchi, da Malam Dikko Umaru Raɗɗa na jihar Katsina.
Sauran su ne, Dauda Lawal na Zamfara, Abdullahi Sule na Nasarawa, Ahmad Aliyu na Sakkwato, da umar Namadi na jihar Jigawa.
Bugu da ƙari, mataimakan gwamnonin jihohin Kaduna, Delta, Kano, Filato, Ebonyi, da jihar Benuwai, suna cikin waɗanda aka hanga sun kama wuri sun zauna a ɗakin taron.
Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima Ya Gana da Jakadan Burtaniya a Najeriya
A wani rahoton na daban kun ji cewa Shettima ya gana da jakadan Burtaniya a Najeriya a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Bayan fitowa daga ganawar jakadan Burtaniya, Mista Montgomery, ya shaida wa yan jarida cewa sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ƙasahen biyu.
Asali: Legit.ng