Gwamnan PDP Ya Shiga Matsala Yayin Da Shugaban NYSC Zai Bayar Da Shaida a Gaban Kotu
- Shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed, ya shirya bayar da shaida a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Enugu
- Ana zargin gwamnan PDP Peter Mbah na jihar Enugu da gabatar da satifiket ɗin bogi na NYSC a lokacin babban zaɓen 2023
- Hukumar NYSC ta sha musanta cewa ta ba gwamnan sarifiket ɗin kammala hidimtawa ƙasa saɓanin iƙirarin da Mbah yake an ba shi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Enugu - Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yana cikin tasku kan taƙaddamar satifiket da yake yi da hukumar yi wa ƙasa hidima ta (NYSC).
Hakan na zuwa ne bayan shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed ya shirya bayyana a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Enugu, domin bayar da shaida akan satifiket ɗin NYSC da Mbah ya gabatar.
Dalilin da yasa shugaban NYSC zai bayar da shaida akan gwamna Mbah na jihar Enugu
Hukumar talabijin ta ƙasa (NTA) ita ce ta sanar da bayar da shaidar da shugaban na NYSC zai yi a shafinta na Twitter a safiyar ranar Alhamis, 22 ga watan Yunin 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan ba a manta ba dai batun satifiket ɗin kammala NYSC da Mbah ya gabatarwa da INEC kafin babban zaɓen 2023 ya zama abin magana bayan hukumar ta bayyana cewa satifiket ɗin ba daga wajenta ya fito ba.
Chris Ekemezie, lauyan da yake kare gwamnan a ƙarar, a wata hira da Channels TV, ya haƙiƙance cewa gwamnan baya da wani dalili da zai sanya ya yi ƙaryar satifiket ɗin sannan ya yi mamakin yadda hukumar ta musanta bayar da satifiket ɗin ya fito daga wajenta.
Karin Bayani: Shettima Ya Sa Labule da Bill Gates, Ɗangote da Wasu Gwamnoni a Villa, Bayanai Sun Fito
Ekemezie ya yi bayanin cewa gwamna Mbah ya yi bautar ƙasarsa ne a jihar Legas.
Ya ƙara da cewa gwamnan ya jingine bautar ƙasar tasa na wata shida domin zuwa makarantar lauyoyi amma ya dawo daga baya ya kammala.
NYSC Ta Musanta Ba Mbah Satifiket
Rahoto ya zo kan yadda hukumar bautar ƙasa (NYSC) ta jefa gwamnan jihar Enugi, Peter Mbah a cikin matsala bayan ta musanta ba shi takardar satifiket ɗin kala bautar ƙasa.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa basu san inda gwamnan ya samo satifiket ɗin da yake yawo da shi a matsayin shaidar kammala bautar ƙasa ba.
Asali: Legit.ng