“Shin Ta Mutu Ne?” Hotunan Matashiya Tsugune Da Zobe a Hannu Ya Yadu, Ta Nemi Auren Saurayinta

“Shin Ta Mutu Ne?” Hotunan Matashiya Tsugune Da Zobe a Hannu Ya Yadu, Ta Nemi Auren Saurayinta

  • Maimakon ta jira sai namiji ya nemi aurenta, wata matashiya ta tauna tsakuwa inda ta yi abun mamaki
  • Ba tare da ta damu da diramar da ta haifar ba, matashiyar ta durkusa kan gwiwowinta a taron jama'a domin neman auren saurayinta
  • Hotuna daga taron neman auren mai ban mamaki, da kuma yanayin saurayin nara ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

Kamar yadda yake bisa al'adar mutane da dama, namiji ko saurayi ne yake neman auren budurwarsa amma wata matashiya ta yanke shawarar sauya al'adar.

A hotuna da ke yawo, an gano matashiyar tsugune a gaban saurayinta a bainar jama'a rike da zobe a hannunta.

Matashiya ta nemi auren saurayinta
“Shin Ta Mutu Ne?” Hotunan Matashiya Tsugune Da Zobe a Hannu Ya Yadu, Ta Nemi Auren Saurayinta Hoto: Maazi Ogbonnaya Okoro II
Asali: Facebook

Jama'a da suka taru sun cika da mamaki, inda aka nadi hotunan yanayinsu, yayin da matashiya ta rike hannun saurayin nata.

Daga nan sai ta sanya masa zoben alkawari sannan ta nuna sa ga duniya. Saurayin na ta murmushi yayin da ya ke haska zoben nasa.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Gintse Aurenta Na Shekaru 14 Da Mijinta, Ta Bayar Da Dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shirya dirama, Maazi Ogbonnaya Okoro II, wanda ya wallafa hotunan a Facebook, ya bayyana cewa yadda budurwar ta yi shine yadda ya kamata ya kasance.

Ba a tabbatar da sahihancin baikon ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Jama'a sun yi martani

Chibuikem Oguike ya ce:

"A nawa ra'ayin kada wanda ya durkusa a gaban wani."

Johnson Chidinmma Priscilla ta ce:

"Bari na je na siya zobe."

Asa Bathsheba ta ce:

"Idan aka bari mata suka fara neman auren maza, babu namiji ko guda da zai rage."

Ijaga Nwagada Onyekachi DanFrank ya ce:

"Kuma abun mamaki yarinyar bata mutu ba faaaa.
"Na taya su murna."

Elijah Oghenewero Jnr ya ce:

"Mutumin shine dai tukwicin, amma da nine a matsayinsa, da na karbi zoben daga wajenta sannan na nemi aurenta, amma yana nan yadda yake."

Kara karanta wannan

Amarya Ta Kai Ango Ƙara Kotu, Ta Nemi a Raba Auren Saboda Yana da Matsalar Ruwan Kwayar Halitta

Matashiya ta baje kolin kayayyakin da ta siyo a kasuwa, ta kaso N180k

A wani labari na daban, wata matashiya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta baje kolin kayan da ta siyo a kasuwa.

Matashiyar ta je kasuwa don siyan kayan amfanin gida amma sai da ta murkushe kudi har naira 180k wajen siyan kayayyaki daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng