Daga Kan Louis Edet Zuwa Kayode Egbetokun: Jerin Sunayen Shugabannin Yan Sanda Tun Bayan Samun Yanci

Daga Kan Louis Edet Zuwa Kayode Egbetokun: Jerin Sunayen Shugabannin Yan Sanda Tun Bayan Samun Yanci

A ranar Litinin, 19 ga watan Yuni ne shugaban kasa Bola Tinubu ya nada DIG Kayode Egbetokun, a matsayin mukaddashin shugaban rundunar yan sandan Najeriya (IGP).

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shugaban kasar ya nada Egbetokun a matsayin sabon shugaban yan sandan bayan yi wa tsohon shugaban yan sanda, Usman Alkali Baba ritaya.

Shugabannin yan sanda
Daga Kan Louis Edet Zuwa Kayode Egbetokun: Jerin Sunayen Shugabannin Yan Sanda Tun Bayan Samun Yanci Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yayin da ake jiran majalisar dokokin tarayya ta tabbatar da Egbetokun, zai zama shine sufeto janar na yan sanda na 22 tun bayan karban yancin kai idan har yan majalisar suka amince da shi.

Bayan Tinubu ya nada sabon shugaban yan sanda, Legit.ng ta lissafo jerin shugabannin rundunar soji da Najeriya ta yi tun 1960 da jihohi da yankunansu.

Jerin sunayen Shugabannin yan sanda da aka nada tun samun yanci

1. IGP Louis Edet (1964-1966), Calabar, jihar Cross River, kudu maso kudu

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sabon Shugaban Yan Sandan Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan Bayan Gaje Baba

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2. IGP Kam Salem (1966-1975), Dikwa, jihar Borno state, arewa maso gabas

3. IGP Muhammadu Dikko Yusufu (1975-1979) Katsina, jihar Katsina, Katsina, arewa maso yamma

4. IGP Adamu Suleiman (1979–1981), Yola, jihar Adamawa, arewa maso gabas

5. IGP Sunday Adewusi (1981–1983), Oyo, jihar Oyo, kudu maso yamma

6. IGP Etim Inyang (1985–1986), jihar Akwa-Ibom, kudu maso kudu

7. IGP Muhammadu Gambo-Jimeta (1986–1990), Yola, jihar Adamawa, arewa maso gabas

8. IGP Aliyu Atta (1990–1993), Kogi, jihar Kogi state, arewa ta tsakiya

9. IGP Ibrahim Coomassie (1993–1999), Katsina, jihar Katsina, arewa maso yamma

Sufeto Janar na yan sandan Najeriya: 2000 zuwa 2010

10. IGP Musiliu Smith (1999–2002), jihar Lagos, kudu maso yamma

11. IGP Mustafa Adebayo Balogun (2002 – 2005), jihar Osun, kudu maso yamma

12. IGP Sunday Ehindero (2005–2007), jihar Ondo, kudu maso yamma

13. IGP Mike Mbama Okiro (2007–2009), Imo, kudu maso gabas

Kara karanta wannan

PDP Ta Shiga Tangal-Tangal, Shugabanni 7 da Suka Yi Murabus Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

14. IGP Ogbonna Okechukwu Onovo (2009 - 2010), Enugu, kudu maso gabas

Sufeto Janar na yan sandan Najeriya: 2010 zuwa yanzu

15. IGP Hafiz Ringim (2010 - 2012), Jigawa, arewa maso yamma

16. IGP Mohammed DIKKO Abubarkar (2012 - 2014), Sokoto, arewa maso yamma

17. IGP Suleiman Abba (2014 -2015), Jigawa, arewa maso yamma

18. IGP Solomon E. Arase (2015 - 2016), Edo, kudu maso kudu

19. IGP Ibrahim Kpotun Idris (2016-2019), Niger, arewa ta tsakiya

20. IGP Mohammed Abubakar Adamu (2019-2021), Nasarawa, arewa ta tsakiya

21. IGP Usman Alkali Baba (2021-2023), Geidam, jihar Yobe, arewa maso gabas

22: Mukaddashin IGP Kayode Egbetokun, jihar Ogun, kudu maso yamma

Dalilin da yasa shugaban rundunar sojin ruwa mai barin gado bai mika shugabanci ga magajinsa ba

A wani labarin kuma, mun ji cewa hedkwatar rundunar sojin ruwa ta karyata zargin cewa shugaban rundunar mai barin gado, Awwal Gambo, ya ki mika mulki ga magajinsa, Emmanuel Ogalla.

Kara karanta wannan

Janar Taoreed Abiodun Lagbaja: Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Hafsan Sojoji

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, daraktan labarai na rundunar sojin ruwa, Adedotun Ayo-Vaughan, mika mulki ga wani a rundunar soji yana da tsari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng