RMAFC Ta Musanta Batun Karin Albashi Ga Tinubu, Shettima, Da Sauransu, Ta Ce Akwai Sauran Lokaci
- Hukumar tattara kuɗaɗen shiga da lura da kasafin kudi (RMAFC), ta musanta labarin ƙarin albashin manyan 'yan siyasa da aka ce ta yi
- Hukumar ta ce har yanzu ba a gama daddalewa ba a kan batun wanda dole sai shugaban ƙasa da 'yan majalisu sun amince da shi
- Sakataren yaɗa labarai na hukumar, Christian Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai
Hukumar tattara kudaden shiga da lura da kasafin kudi (RMAFC), ta musanta rahoton da ke cewa ta amince da ƙarin albashin 'yan siyasa da ma'aikatan ɓangaren shari’a da kashi 114%.
A wata tattaunawa ta musamman da jaridar Leadership, jami’in hulda da jama’a na hukumar RMAFC, Christian Nwachukwu, ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu bai kai ga amincewa da ƙarin albashin ba tukun.
Babbar kwamishiniyar tarayya a hukumar Rakiya Tanko-Ayuba ce ta bayyana batun ƙarin albashin a lokacin da ta wakilci shugaban RMAFC, Mohammad Shehu, wajen gabatar da rahoton ƙarin albashi ga gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ranar Talata a Birnin Kebbi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rakiya ta ce an fara aiwatar da shirye-shiryen biyan kuɗaɗen da aka ƙara tun daga ranar 1 ga Janairun 2023, iƙirarin da kakakin hukumar ya musanta.
Shugaban ƙasa bai sanyawa ƙudirin hannu ba
Nwachukwu ya ce ba su kai ga yin maganar ba saboda har yanzu shugaban ƙasa bai sanyawa ƙudirin hannu ba.
Ya ce duk da cewa akwai maganar ƙarin albashin a ƙasa, hakan ba hana nufin ya zama doka ba, tunda har yanzu shugaban ƙasa bai kai ga amincewa da ƙarin ba.
Ya ƙara da cewa kafin shirin ya kammala, dole ne sai an aikawa 'yan Majalisun Tarayya sun duba, idan sun amince da shi, sai a turawa shugaban ƙasa, idan ya amince shikenan shirin ya tabbata.
'Yan Najeriya sun yi tsokaci game da labarin
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakunansu a lokacin da labarin ƙarin albashin manyan 'yan siyasan da kashi 114% ya fita.
Daga ciki akwai tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani da ya ce kamata ya yi a fara da ƙarawa ƙananun ma'aikata albashi kafin a zo kan na 'yan siyasa.
Makomar tsofaffin gwamnoni a gwamnatin Tinubu
Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a baya da ke nuni da cewa, Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin ganin bai cika majalisar ministocinsa da tsofaffin gwamnonin jihohi ba.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da manyan 'yan siyasa daga jihohi, ciki har da tsofaffin gwamnonin ke ta hanƙoron ganin sun shiga cikin jerin ministocin na Tinubu.
Asali: Legit.ng