Manyan Mutane Sun Fi Talakawan Najeriya Jin Radadin Tsadar Man Fetur, Tsohon Dan Majalisa
- Jigon jam'iyyar APC, Musa Adar ya magantu a kan kokawar da talakawa ke yi dangane da cire tallafin man fetur
- Adar wanda ya kasance tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Gada-Goronyo a jihar Sokoto ya ce manyan mutane sun fi talakawa shan wahalar tsadar man
- A cewarsa, manyan mutane sun fi talakawa siyan mai domin wasun su sun mallaki motoci kusan 10
Tsohon dan majalisar wakilai, Musa Adar, ya ce karin farashin man fetur da aka yi sakamakon cire tallafin man fetur ya fi shafar manyan mutane fiye da talakawan Najeriya.
Mista Adar, wanda ya wakilci mazabar Gada-Goronyo a jihar Sokoto tsakanin 2007 da 2023, ya magantu ne lokacin da ya bayyana a shirin safe na Arise TV, a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni.
Ku tuna cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur yayin gabatar da jawabin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Lamarin ya haifar da kara farashin man fetur zuwa fiye da N500 a gidajen mai a fadin kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Manyan mutane sun fi talakawa siyan man fetur, Adar
Da yake magana kan korafin da yan Najeriya ke yi saboda hawan farashin ma fetur, Mista Adar ya ce abun ya fi shafar manyan mutane fiye da talakawan Najeriya saboda sun fi kowa siyan man fetur, Premium Times ta rahoto.
Adar ya ce:
"Manyan mutane ake tallafawa da farashin man fetur na baya, ba talakawa ba, kamar yadda wasu mutane ke kokarin mayar da abun.
"Yawancin masu mota da manyan mutane sune masu kudi inda muke mallakar motoci, daya, biyu, uku, hudu, biyar da ma goma, musamman a gwamnati inda za ka ga ayarin ministoci da masu tsaronsa da motoci fiye da 20 a lokaci guda."
Dan majalisar, wanda ya kasance dan jam'iyyar APC mai mulki ya fadi zabe a kokarinsa na yin tazarce inda ya sha kaye a hannun abokin adawarsa na PDP mai shekaru 33, Bashir Gorau a zaben 2023.
Yan Najeriya da dama, ciki harda yan majalisar wakilan kasar sun soki Tinubu kan rashin samar da kayan rage radadi kafin cire tallafin man.
Sakamakon kokawar da jama'a suka yi, shugaban NNPPC, Mele Kyari, ya sanar a ranar 1 ga watan Yuni cewa Tinubu ya ba da umurnin bayar da tallafi domin ragewa mutane radadin tsadar farashin man.
Sai dai kuma, har yanzu kimanin makonni uku kenan babu wani nmataki da aka aiwatar.
Yan Najeriya za su samu labari mai dadi daga Tinubu da zaran ya dawo daga Faransa
Da aka tambaye shi game da dalilin da yasa Tinubu bai tanadi kayan rage radadi kafin cire tallafin ba, Mista Adar ya ce shawarar da shugaban kasar ya yanke kwatsam domin gujewa guggun masu sukar manufar ne.
Ya kara da cewar Tinubu, wanda ya bar Najeriya zuwa kasar Faransa a ranar Talata zai baiwa yan Najeriya labari mai dadi game da tallafin da dawowarsa.
Ya ce:
"Ana aiki kan kayan rage radadi. Kuma nan ba da jimawa ba, idan shugaban kasar ya dawo daga Faransa, ina ba yan Najeriya tabbacin za su samu labari mai dadi."
Godwin Emefiele: Jigon APC ya nemi Tinubu ya binciki Sanusi
A wani labari na daban, mun ji cewa jigon APC, Kailani Muhammad, ya shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya fadada binciken da ke gudana a ofishin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele har zuwa zamanin Sanusi Lamido.
Kailani ya bukaci shugaban kasa Tinubu da kada ya damu da ziyarar da tsohon sarkin Kanon ya kai masa, yana mai bayyana su a matsayin dabarun neman jan hankali.
Asali: Legit.ng