Zanga-Zanga Ta Barke a Jami'ar Jihar Ondo Kan Korar Ma'aikata 30
- Ma'aikata sun fita zanga-zanga a jami'ar kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin jihar Ondo (OAUSTECH)
- A cewar wasu daga cikin masu zanga-zangar, ba zasu bari a ci gaba da harkokin makarantar ba har sai an yi abinda suke buƙata
- Sun bayyana cewa sun fara wannan zanga-zanga ne domin nuna adawa da matakin korar wasu ma'aikata 30
Ondo - Jami'ar kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin jihar Ondo (OAUSTECH) da ke Okitipupa, ta kori ma'aikata 30 daga bakin aiki, kamar yadda rahoton Daily Trust ya kawo.
Fusatattun ma'aikatan jami'ar ne suka tabbatar da haka ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, 2023 yayin da suka fara zanga-zangar adawa da korar abokan aikinsu wanda suka ce an yi ba kan ƙa'ida ba.
Masu zanga-zangar sun toshe babbar kofar shiga makarantar, kuma hakan ya kawo cikas ga harkokin karatu da kasuwanci a jami'ar na tsawon awanni.
Haka nan masu zanga-zanga sun hana kowace mota ko mutane shiga harabar makarantar, sun kuma zargi shugabannin jami'ar karkashin Farfesa Akinbo Adesomoju da korar ma'aikatan guda 30.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa jami'ar ta kori ma'aikatan?
Wasu daga cikin tawagar yan zanga-zangar sun shaida wa jaridar cewa waɗanda aka kora halastattun ma'aikata ne da jami'a ta ɗauka kuma har an ba su takardar ɗaukar aiki.
Sun ƙara da cewa sun sha mamakin yadda aka ɗauki ma'aikatan aiki watanni kaɗan da suka shige amma ranar Talata aka raba musu takardar kora daga aiki.
"Sun tsallake duk wani mataki har an basu takardar ɗaukar aiki. Sun yi wa jami'a aiki tsawon watanni shida (ma'aikatan da aka kora)," inji ɗaya daga cikin masu zanga-zanga.
Ma'aikatan sun lashi takobin dakatar harkokin karatu da kasuwanci a jami'ar har sai an maida 'yan uwansu da aka kora. Sun kira korar ma'aikatan da cin amanar aiki.
Zamu maida martani - Adeagbo
Yayin da aka tuntube shi, mai magana da yawun jami'ar, Paul Adeagbo, bai musanta korar ma'aikatan ba kuma bai tabbatar ba, Punch ta rahoto.
Adeagbo ya ce hukumar makaranta zata maida martani kan lamarin nan gaba kaɗan. Amma har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga jami'ar.
Sabon IGP Ya Shiga Ofis, Ya Karbi Ragamar Yan Sandan Kasar Nan
A wani labarin kuma sabon Sifetan yan sanda IGP ya kama aiki gadan- gadan, ya karɓi gagama daga Usman Baba.
Egbetokun, ya zama shugaban rundunar yan sanda ta ƙasa na 22 a tarihin bayan naɗin da shugaban kasa, Bola Tinubu, ya masa.
Asali: Legit.ng