"Ba Ka Amfane Mu Da Komai Ba": Babban Basarake Ya Caccaki Tsohon Ministan Buhari

"Ba Ka Amfane Mu Da Komai Ba": Babban Basarake Ya Caccaki Tsohon Ministan Buhari

  • Babban basaraken masarautar Benin a jihar Edo ya caccaki tsohon ƙaramin ministan kasafin kuɗi na ƙasar nan
  • Oba Ewuare II ya bayyana cewa Prince Clem Agba bai amfane su da komai ba a muƙamin da ya riƙe na minista
  • Basaraken ya bayyana cewa duk da ya taimaka wajen samun muƙaminsa, tsohon ministan na ɗarewa kan kujerar kawai sai ya guje su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Edo - Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya caccaki tsohon ƙaramin ministan kasafin kuɗi na ƙasa, Prince Clem Agba, bisa ƙin amfanar da al'ummar Benin daga muƙaminsa.

Oba Ewuare II ya ce duk da sai da ya sanya baki sannan Agba ya samu muƙamin minista, yana hawa kujerar kawai sai ya manta da kowa, cewar rahoton Leadership.

Oba Ewuare II ya caccaki tsohon ministan Buhari
Tsohon karamin ministan kasafin kudi, Prince Clem Agba Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

Babban basaraken ya bayyana cewa Agba yana ɗarewa kan kujerar bai fi ko sau ɗaya zuwa sau biyu suka sake sanya shi a idanunsu.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina tunanin gaba ɗaya lokacin da kake kan muƙaminka, ba zan iya tuna cewa mun sanya ka idanuwanmu fiye da sau biyu ba. Na farko lokacin da ka zo domin ƙorafi kan ambaliyar da aka samu a Benin sannan na biyu yanzu da wa'adin mulkinka ya ƙare."

Babban basaraken ya yi silar zamansa minista

"Mun tattauna da kai jefi-jefi, sannan tabbas sanya bakin da na yi wajen tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sanya ka amfana daga ofishin da ka riƙe. Mu na yi wa Allah godiya a bisa hakan."
"Amma kuma ina mamakin abubuwa da dama, a yayin da ka amfana da wannan muƙamin, bana tunanin akwai wani daga cikin mutanen mu da ya amfana da muƙamin da ka riƙe."
"Ina faɗin cewa su gode maka idan akwai wanda ya taɓa amfana da zaman da aka yi a matsayin minista."

Kara karanta wannan

Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Ya Ba Wa Peter Obi Shawarar Abin Da Ya Dace Ya Yi Wa Tinubu

Agba dai ya je fadar basaraken ne domin ya bayyana shirinsa na bayar da gudunmawa ga gidan adana kayan tarihi na Benin, bayan ba wani abu zai iya taɓukawa ba tun da ya bar ofis, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Majalisar Dokokin Jihar Edo Ta Yi Sabon Kakaki

A wani labarin na daban kuma, mambobin majalisar dokokin jihar Edo sun zaɓi sabon kakakin majalisar wanda zai ci gaba da jan ragamarta.

Mambobin majalisar sun zaɓi Blessing Agbebaku a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin. Haka kuma ƴan majalisar sun zaɓi ƴar majalisa mace a matsayin mataimakiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng