Shugaba Bola Tinubu: Tafiyar Farko Zuwa Kasar Waje Da Shugabannin Najeriya Suka Yi Tun Daga Shekarar 1999

Shugaba Bola Tinubu: Tafiyar Farko Zuwa Kasar Waje Da Shugabannin Najeriya Suka Yi Tun Daga Shekarar 1999

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa ƙasar Faransa kwanaki 23 bayan ya karɓi mulki a hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Tafiyar ta Tinubu ta ba baƙon abu bane domin ba shi bane shugaban ƙasa na farko wanda ya fara shilla wa ƙasar waje kwanaki kaɗan bayan ya hau mulki
  • Wata sabuwar ƙididdiga ta nuna cewa shugabannin ƙasar nan daga shekarar 1999 sun sha shilla wa zuwa ƙasashen wajen kwanaki kaɗan bayan hawansu mulki

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa ƙasar Faransa bayan kwanaki 23 da hawa kan karagar mulkin ƙasar nan.

Shugaban ƙasar zai halarci wani taro ne a ƙasar kan tattalin arziƙi wanda zai gudana a ranakun 22 da 23 na watan Yunin 2023.

Lokacin farko da shugabannin Najeriya suka yi tafiya zuwa kasar waje
Shugaban kasa Bola Tinubu lokacin da ya isa kasar France Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban ƙasar kan ayyuka na musamman da watsa labarai, Dele Alake, ya fitar a ranar Litinin, 19 ga watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

"Allah Ba Zai Ɗora Mana Abinda Ba Zamu Iya Ba" Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali a Masallacin Idi

Meyasa Shugaba Tinubu ya bar Najeriya kwanaki kaɗan bayan ya hau mulki

Tinubu ya fita zuwa ƙasar nan a matsayin shugaban ƙasa a karon farko kwanaki 23 bayan ya hau kan mulki. An rantsar da shi ne dai a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Tinubu ya ƙarbi mulki ne a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a hannun tsohon Shugaba Muhammadu Buhari bayan ya kwashe shekara takwas akan mulki.

Tinubu, Buhari, da sauran shugabannin Najeriya tun daga shekarar 1999 da suka yi tafiya zuwa ƙasar waje kwanaki kaɗan bayan hawa mulki.

A wani rubutu da tsohon hadimin Shugaba Buhari, Tolu Ogunlesi, ya yi a Twitter, ya nuna cewa shugabannin ƙasar nan tun daga shekarar 1999, sun sha barin ƙasar nan a cikin watan farko bayan hawa mulki.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu Da Sauran Manyan Jiga-Jigan Da Suka Tarbi Shugaba Tinubu a Legas

Ga jerin kwanakin da suka ɗauka kafin tafiya zuwa ƙasar waje a cewar Ogunlesi:

Olusegun Obasanjo: 15 ga watan Yunin 1999, rantsar da Thabo Mbeki.

Umaru Musa Yar'Adua: 6 ga watan Yunin 2007, taron G8 a ƙasar Germany.

Goodluck Jonathan (a matsayin shugaban riƙon ƙwarya): 11 ga watan Afirilun 2010, ƙasar Amurka taron makamashin nukiliya.

Muhammadu Buhari: 3 ga watan Yuni 2015, Nijar, Chad

Bola Tinubu: 20 ga watan Yunin 2023, ƙasar Faransa taron tattalin arziƙi.

Ga rubutun nasa nan ƙasa:

Shugaba Tinubu Ya Isa Kasar Faransa

A wani labarin kuma, jirgin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa ƙasar Faransa domin halartar taron tattalin arziƙi da za a gudanar a ƙasar.

Shugaban ƙasar ya bar Najeriya ne domin halartar taron wanda za a gudanar a ranakun Alhamis da Juma'a. Ana sa ran zai dawo gida ranar Asabar, 24 ga watan Yunin 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng