Sabon IGP, Egbetokun Ya Yi Magana Kan Yadda Yake Ji Dangane Da Mukamin Da Aka Ba Shi
- Sabon babban sufetan rundunar ƴan sandan Najeriya, ya bayyana cewa yana jinsa kamar wani zaki wanda zai murƙushe maƙiyan ƙasar nan
- Kayode Egbetokun wanda aka ba muƙamin a matsayin na riƙon ƙwarya ya nuna shirinsa na fatattakar duk wasu masu laifi
- An naɗa Egbetokun a muƙamin ne domin maye gurbin Usman Baba Alkali wanda Shugaba Tinubu ya sallama daga muƙamin IGP
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Babban sufetan rundunar ƴan sanda na riƙon ƙwarya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa yana jinsa kamar zaki wanda ya shirya murƙushe maƙiyan Najeriya.
Jaridar Daily Trust tace ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan mataimakin shugaban ƙasa ya sanya masa ƙwalliyar kama aiki a gaban matarsa, Mrs Egbetokun, a wani ɗan ƙaramin biki a ɗakin taro na mataimakin shugaban ƙasar.
Bikin ya samu halartar tsohon IGP, Usman Alkali Baba, mai bada shawara ka harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.
Tsohon Sufetan 'Yan Sanda, Usman Baba Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Korarsa Daga Aiki Da Shugaba Tinubu Ya Yi
An naɗa Egbetokun wanda tsohon mataimakin sufetan ƴan sanda ne mai kula da yankin Kudu maso Yamma, a ranar Litinin domin maye gurbin Usman Baba, cewar rahoton Tribune.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya shirya fatattakar masu aikata laifi
Da yake amsa tambayoyi wajen manema labarai bayan kammala bikin, sabon IGP ɗin ya bayyana shirinsa na murƙushe dukkanin wasu masu laifi da maƙiyan ƙasar nan.
Da aka tambayesa ko ya yake jin ɗauyin da aka ɗora masa yanzu, sai ya kada baki yace:
"Yanzu an yi min kwalliya sannan ina hangen fara aiki gadan-gadan gobe da misalin ƙarfe 11:00 na safe. Ba zan iya gaya muku haƙiƙanin yadda na ke ji ba, amma idan zan gaya muku wani abu, zan gaya muku cewa inajin kamar wata damisa a jikina, a shirye domin fatattakar dukkanin masu laifi a Najeriya."
"Sannan a wani lokaci ina jin kamar zaki a jikina a shirye domin murƙushe dukkanin maƙiyan cikin gida na Najeriya. Haka nake ji na yanzu."
Usman Baba Ƴa Yi Magana Bayan Rasa Mukaminsa
A wani labarin, tsohon sufetan rundunar ƴan sandan ƙasar nan, ya yi magana bayan korarsa da Shugaba Tinubu ya yi daga kan muƙaminsa.
Usman Baba Alƙali ya bayyana cewa bai damu ba ko kaɗan domin haka aikin na su ya gada, ba dawwama ake ana yi ba.
Asali: Legit.ng