Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar Godwin Emefiele Ranar 13 Ga Watan Yuli

Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar Godwin Emefiele Ranar 13 Ga Watan Yuli

  • Gwamnan CBN da shugaban ƙasa ya dakatar, Godwin Emefiele, zai san makomarsa ranar 13 ga watan Yuli, 2023
  • Emefiele ya kai gwamnatin tarayya ƙara Kotu inda ya nemi ta umarci jami'an tsaro su ba shi yancin walwala da zirga-zirga
  • Kusan makonni biyu da suka shige, Tinubu ya dakatar da Emefiele daga matsayin gwamnan CBN kuma DSS ta yi ram da shi

FCT Abuja - Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, na dab da sanin makomarsa kan ƙarar da ya shigar gaban Kotu.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kotun ta shirya yanke hukuncin kan tsare Emefiele da hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) ta yi ranar 13 ga watan Yuni, 2023.

Dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar Godwin Emefiele Ranar 13 Ga Watan Yuli Hoto: Godwin Emefiele
Asali: UGC

Idan baku sha'afa kusan mako biyu da suka shige, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Emefiele daga matsayin gwamnan CBN kuma ya umarci a bincike shi.

Kara karanta wannan

DSS Ta Bankado Wata Kulla-Kulla Da Ake Shiryawa Gwamnatin Tarayya Kan Tsare Emefiele, Bayanai Sun Fito

Sai dai jim kaɗan bayan dakatar da shi, jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya suka damƙe shi domin gudanar da bincike kan zargin da suke masa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan tun da ya shiga hannun DSS, Emefiele ya ci gaba da zama hannun jami'an hukumar ba tare da gurfanar da shi a gaban Kotu ba kusan mako biyu kenan.

Dakataccen gwamnan CBN ya kai ƙara Kotu domin ganin iyalansa

Bisa haka ne Godwin Emefiele ya garzaya babbar kotun birnin tarayya Abuja ta hannun lauyansa, Chief Joesph Daudu, (SAN), domin neman umarnin a barshi ya riƙa ganawa da iyalansa da lauyoyinsa.

A makon da ya gabata, Kotun ta amince da buƙatar Emefiele, inda ta umarci DSS ta bar shi ya riƙa ganawa da iyalansa da kuma lauyoyinsa domin yana da 'yanci.

Bayan nan Emefiele ya nemi Kotun ta umarci jami'an tsaro su ba shi caikken 'yancinsa na zirga-zirga da walwala kamar kowa domin babu dalilin tsare shi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

Yaushe Kotun zata yanke hukuncin kan karar da Emefiele ya shigar?

Bayan sauraron lauyoyin kowane ɓangare game da batun ci gaba da tsare Emefiele ranar Talata, Kotun ta saka ranar 13 ga watan Yuli, 2023 domin yanke hukunci, kamar yadda Vanguard rahoto.

EFCC Ta Titsiye Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom

A wani labarin na daban hukumar EFCC ta titsiye tsohon gwamnan jihar Benuwai kuma babban jigon jam'iyyar PDP, Samuel Ortom.

Mista Ortom ya shiga harabar ofishin EFCC da ke layin Alor Gardon a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai a motarsa da misalin ƙarfe 10:08 na safiyar ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262