Tsohon Sufetan 'Yan Sanda Ya Yi Magana Kan Korarsa Daga Aiki Da Shugaba Tinubu Ya Yi
- Tsohon sufetan rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Usman Alkali Baba, ya yi tsokaci kan korar da shugaba Tinubu ya yi masa daga muƙaminsa
- Usman Baba ya bayyana cewa ko kaɗan bai ji takaicin hukuncin Shugaba Tinubu ba saboda dama haka aikin ya gada
- Tsoshon sufetan ya ce yana da tabbacin magajin nasa zai ɗora daga inda ya tsaya wajen shugabancin rundunar ƴan sandan yadda ya dace
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Tsohon babban sufetan rundunar ƴan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya bayyana cewa bai ji zafin korar da shugaba Tinubu ya yi masa ba daga muƙaminsa, cewar rahoton Premium Times.
Shugaba Tinubu dai a ranar Litinin ya bayar da umarnin ritayar dole ga Usman Baba tare da sauran hafsoshin tsaro. An maye gurbin tsohon babban sufetan da mataimakin sufetan ƴan sanda, Kayode Egbetokun.
Tsohon sufetan ƴan sandan ya yi magana kan cire shi da aka yi daga kan muƙaminsa, a ranar Talata lokacin da ya miƙa ragama shugabanci a hannun Egbetokun.
Ya bayyana cewa yanayin aikin na su dama haka yake idan kai ne yau gobe dole za ka matsa wani ya ci gaba daga inda ka tsaya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa:
"Dama waje ne, ka zo ka yi aiki sannan ka tafi. Ina farin cikin cewa ina miƙa ragama a hannun wanda na san zai ɗora daga inda na tsaya a fannin shugabanci."
Usman Baba ya bayyana irin sanin da ya yi wa magajinsa
Da aka tambaye shi ko ya san wani abu dangane da magajin nasa, Alkali ya bayyana cewa:
"Mun taso tare a cikin aikin, a tare mu ka taso, na taɓa zama shugabansa a wani lokaci har zuwa lokacin da na ke IGP. Ya yi aiki a ƙarƙashi na har sau biyu. Mun yi aiko tare kuma nasan cewa zai ci gaba daga inda na tsaya wajen jan ragamar rundunar ƴan sanda."
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabbin Hafsoshin Tsaro
Rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami hafsoshin tsaro daga muƙaminsu inda ya maye gurbinsu da sabbi.
Shugaban ƙasar ya kuma sauke babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, Usman Alkali Baba daga muƙaminsa, inda ya maye gurbinsa da shugaba na riƙon ƙwarya.
Asali: Legit.ng