Rashin Tsaro: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Manajar Banki, Sun Dade Suna Yi Mata Gargadi

Rashin Tsaro: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Manajar Banki, Sun Dade Suna Yi Mata Gargadi

  • Masu garkuwa sun sace wata manajar daya cikin bankunan Najeriya a akan hanyar Sani Abacha daf kwanan PDP a birnin Yenagoa
  • Wanda aka sacen, Nneka Unoka Ugonochie ta na kan hanyarta na zuwa aiki ne lokacin da 'yan bindigan suka kama ta
  • 'Yan bindigan sun yi shigar bultu da kayan sojoji lokacin da suka sace manajar bankin a daidai inda jami'an tsaro suke tsayuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bayelsa - 'Yan bingiga sun yi garkuwa da wata manajar banki a Najeriya Mrs Nneka Unoka Ugonochie a jihar Bayelsa.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni a kan hanyar Sani Abacha da ke birnin Yenagoa.

Masu garkuwa sun sace manajar bankin Sterling a Bayelsa
Dan Bindiga Mai Garkuwa Da Mutane A Najeriya. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya ba wa mutane mamaki ganin yadda da jami'an tsaro ke zube a wurin amma suka samu damar sace matar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbe Wani Da Ya Yi Niyyar Tserewa Daga Komarsu, Matashin Ya Tsira Da Raunuka A Kaduna

'Yan bindigan sun sha yiwa manajar bankin kashedi

Wata majiya ta tabbatar cewa 'yan bindigan sun dade suna yi wa matar kashedi akan cewa ta kaura daga gidanta wanda ke kusa da gidan mai gidansu da aka kama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta tabbatar cewa a baya gamayyar jami'an tsaro ne ke gadin matar kafin daga baya su watse saboda korafi daga matar na tsadar daukar nauyinsu.

An gargadi matar sau da dama akan cewa dole ta zauna cikin shirin ko ta kwana har sai lokacin da gwamnati ta kwace gidan shugaban masu garkuwan.

'Yan sanda sun tabbatar da sace manajar bankin

Mazauna yankin suna zargin sauran wadanda ba a kama daga yaran John Lyon ne ke aikata duk wani sace-sacen mutane a yankin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Romokere Ibani ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi garkuwa da matar lokacin da ta ke tafiya ofishinta.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An yi ram da wasu mazauna Qatar, rikakkun 'yan safarar kwaya a wata jiha

Masu garkuwan sun sace matar ne su hudu a cikin shigar kayan sojoji.

Bakano Ya Yi Garkuwa Da Kansa, Barayi Sun Sace N356k Da Ya Karba Na Fansa

A wani labarin, wani matashi ya yi garkuwa da kansa a jihar Kano tare da karbar kudin fansa.

Matashin mai suna Nafi'u Sulaiman ya karbi kudin fansa har N365,000 daga wurin kawunsa.

Daga bisani ya ce barayi sun sace kudin bayan ya binne kudaden a wani kango don daukar su daga baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.