EFCC Ta Titsiye Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom

EFCC Ta Titsiye Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom

  • Samuel Ortom, tsohon gwamnan jihar Benuwai ya shiga hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC
  • Rahoto ya nuna cewa tun karfe 10:08 na safe tsohon gwamnan ya kai kansa ofishin EFCC kuma har yanzun yana tsare
  • Hukumar ta gayyaci Ortom, babban jigon PDP kuma mamban tawagar G-5 domin ya ama tambayoyi bayan ya bar tulin bashi a asusu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue State - Tsohon gwamnan jihar Benuwai da ya sauka ranar 29 ga watan Mayu, Samuel Ortom, yanzu haka yana tsare a hannun hukumar yaƙi da rashawa EFCC.

Wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro cewa hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, ta gayyaci tsohon gwamnan ne domin amsa wasu tambayoyi.

Tsohon gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.
EFCC Ta Titsiye Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom Hoto: Native reporters/facebook
Asali: Facebook

Mista Ortom ya shiga harabar ofishin EFCC da ke layin Alor Gardon a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai a motarsa da misalin ƙarfe 10:08 na safiyar ranar Talata, 20 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Dalilin da Ya Sa Ya Marawa Akpabio Baya Ya Zama Shugaban Majalisa

Haka nan kuma rahotanni sun bayyana cewa da isarsa, ya fito daga mota sannan ya wuce kai tsaye zuwa cikin ginin ofishin hukumar reshen jihar Benuwai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ga tsohon kakakin tsohon gwamnan, Terver Akase, da tsohon babban mai taimaka masa na musamman kan harkoki na musamman, Abraham Kwanhgu, a tare da Ortom.

Legit.ng Hausa ta fahimci veqa har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoton da misalin karfe 11:25 safe, tsohon gwamnan bai bar ofishin EFCC ba.

Yadda Ortom ya bar tulin bashi a asusun gwamnati

Idan baku manta ba, rahoto ya nuna yadda Samuel Ortom ya bar asusun gwamnatin Benuwai da tulin bashin biliyan N187.7Bn.

A wani ɗan kwarya-kwaryan taron da aka shirya a gidan gwamnatin Benuwai, Ortom ya faɗa wa sabon gwamna, Hyacinth Alia, cewa takardun da ya miƙa masa kashi uku na kunshe da taƙaitaccen bayani kan zango 2 da ya yi.

Kara karanta wannan

Rusau Da Wasu Muhimman Matakai Da Gwamnoni Suka Dauka a Cikin Kwana 20 Da Hawa Mulki

Ortom ya yi bayanin cewa a tsawon shekaru 8 da ya shafe kan madafun iko, Benuwai ta samu kuɗin shiga biliyan N734.9bn zuwa watan Afrilu, 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bugu da ƙari, ya ce ya bar wa sabon gwamnan tulin bashin da ya kai naira biliyan N187.7bn wanda ya kunshi albashin da ma'aikata ke bi bashi, kuɗin fansho, rance da sauransu.

Shugabannin PDP 7 da Suka Yi Murabus, Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

A wani labarin na daban Tsoffin shugabannin PDP 7 a jihar Imo sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.

Gwamnan jihar Imo mai neman tazarce a inuwar APC, Hope Uzodinma, ya karɓe su hannu a biyu a wani taro da aka shirya a fadar gwamnatinsa da ke Owerri, babban birnin jiha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262