Sabon Shugaban Hafsan Sojoji: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Janar Lagbaja
A ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Janar Taoreed Abiodun Lagbaja a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji.
Ana ganin Lagbaja na daya daga cikin janarori mafi kyawu a rundunar sojojin Najeriya kamar yadda jaridar PM News ta rahoto a watan Maris din 2023.
Shugaban kasa Tinubu ya kuma yi nade-nade da dama a rundunar sojin kasar, Channels TV ta rahoto.
Lagbaja ya karbi mulki daga hannun Laftanal Janar Faruk Yahaya, tsohon shugaban hafsan soji wanda ya maye gurbin Ibrahim Attahiru, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama tare da jami'an soji 10 a watan Mayun 2021.
Wanene Taoreed Abiodun Lagbaja?
- Har zuwa sabon nadin da aka yi masa, Lagbaja ya kasance Babban Janar da ke jan ragamar sashi na 1, rundunar sojojin Najeriya, wato GOC a Kaduna.
- A matsayinsa na GOC a Kaduna, Janar Lagbaja ya jagoranci dakaru a yaki da muggan yan fashi da yan ta'adda a Kaduna, Neja, Kebbi, da sauran jihohin arewa maso yamma.
- Lagbaja ya kuma yi aiki a matsayin shugaban sashin ayyuka, hedkwatar rundunar sojoji, Abuja.
- Sabon shugaban hafsan sojin ya fito ne daga Ilobu, wani gari wanda shine hedkwatar karamar hukumar Irepodun na jihar Osun, kudu maso yammacin Najeriya
- Har zuwa nadinsa Lagbaja a matsayin shugaban hafsan soji, lokaci na karshe da dan kudu maso yamma ya rike mukamin ya kasance a 1979 na tsawon watanni shi-wanda Janar Ipoola Alani Akinrinade ya yi. Hakan na nufin shine shugaban hafsan soji na farko daga kudu masu yamma cikin shekaru 43.
- Lagbaja shine shugaban hafsan sojin Najeriya na 23.
Shugaban Kasa Bola Tinubu: Cikakkun Sunayen Hafsoshin Tsaro, Manyan Kwamandojin Fadar Shugaban Kasa Da Sauransu
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jerin sunayen hafsoshin tsaro, IGP, da sauran nade-naden da Tinubu ya yi a hukumar tsaro
A baya mun ji cewa makonni uku da kama aikin shugabancin kasa, shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da yi wa shugabannin tsaro ritaya nan take a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.
Sauye-sauyen ya kuma shafi Sufeto Janar na yan sanda, manyan masu ba da shawara kan tsaro da kuma kwanturola janar na Kwastam yayin da aka sanar da madadinsu wadanda aka umurta da kama aiki a nan take.
Asali: Legit.ng