Yan Daba Sun Addabi Al’ummar Wasu Garuruwa a Jihar Kano, Dan Majalisa Ya Koka

Yan Daba Sun Addabi Al’ummar Wasu Garuruwa a Jihar Kano, Dan Majalisa Ya Koka

  • Al'ummar yankin Dala da ke jihar Kano suna cikin mawuyacin hali saboda hare-haren yan daba
  • Dan majalisa mai wakiltan Dala a majalisar jihar Kano, Lawan Hussaini Dala, ya koka kan yadda yan daba suka addabi al'ummar mazabarsa
  • Ya ce maharan na zuwa su da yawa sannan su yi ta sace-sace, barna da ma halaka wasu ta hanyar caka masu wuka

Kano - Mazauna garuruwa a karamar hukumar Dala ta jihar Kano na zaman dar-dar sakamakon hare-haren da wasu bata gari suka shafe kwanaki shida suka kaiwa a yankin

Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltan garuruwan, Lawan Hussaini Dala (NNPP), shine ya bayyana hakan bayan ya gabatar da wani kudiri yayin zaman majalisar a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.

Taswirar jihar Kano
Yan Daba Sun Addabi Al’ummar Wasu Garuruwa a Jihar Kano, Dan Majalisa Ya Koka Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Hussaini Dala ya ce garuruwan da abun ya shafa suna cikin mawuyacin hali yayin da yan daban suke zuwa su da yawa a kullun kwanan duniya.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce maharan na yi wa mutanen awon gaba da kayayyakinsu tare da yi masu barna da kuma soke bayin Allah.

Dan majalisar ya kara da cewar lamarin ya kai ga har an kashe wasu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Dala wanda ya kasance shugaban masu rinjaye a majalisar, ya ce ya gabatar da kudirin ne don jan hankalin gwamnati saboda ta umurci kwamishinan yan sandan jihar da ya tura jami'ai da magance lamarin.

Jerin garuruwa 6 da ke fuskantar hare-haren yan daba a Kano

Ya lissafa yankunan da abun ya shafa a matsayin garuruwan Dala, Madigawa, Yalwa, Rijiya Biyu, Adakawa da Dogon Nama, yana mai cewa wasu daga cikin mazauna yankin sun fara tserewa zuwa wasu wuraren.

"Wadannan garuruwan da makwabtansu na fuskantar wahalhalu yayin da wadannan yan daba ke zuwa da misalin karfe 7pm suna sace-sace, lalata ababen hawa da caccakar mutane. An rasa wasu rayuka ma.

Kara karanta wannan

“Baba Tinubu Lokacinmu Ne Mu Zama Ministan FCT”: Yan Asalin Abuja Sun Koka

"Yanzu haka da nake maka magana, wasu kasunci na rufewa tun misalin karfe 7pm. Mazauna yankin ma na rufe gidajensu da wuri."

Mataimakin kakakin majalisar, Bello Butu-Butu, ya goyi bayan kudirin inda ya ce akwai bukatar a duba gaba daya lamarin tsaron jihar sannan a magance abun, rahoton Within Nigeria.

Daga bisani majalisar ta amince da kudirin sannan ta dage zamanta zuwa Talata, 20 ga watan Yulin 2023.

Mutane 6 cikin 7 da yan bindiga suka sace a Unijos sun shaki iskar yanci

A wani labari na daban, mun ji cewa shida daga cikin daliban jami'ar Jos bakwai da aka yi garkuwa da su sun samu yanci bayan shafe kwanaki biyu a tsare.

An yi garkuwa da daliban wadanda ke zama a wajen makaranta a daren ranar Laraba a dakunansu da ke yankin Ring Road a karamar hukumar Jos ta arewa da ke jihar Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng