Muhimman Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sa Game Da Sabon Sufeto Janar Na 'Yan Sanda, Egbetokun Olukayode
A daren ranar Litinin ɗin da ta gabata ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban jami’in tsaronsa DIG Egbetokun Olukayode a matsayin sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya na riƙon ƙwarya.
Ya bayyana hakan ne a sanarwar da ya fitar ta dakatar da duka shugabannin tsaro masu ci na ƙasar baki ɗaya.
Wannan dai na zuwa ne bayan watanni uku da hukumar ‘yan sanda ta amince da naɗin Egbetokun a matsayin mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda (DIG), wanda zai wakilci shiyyar Kudu maso Yamma.
DIG Egbetokun ya maye gurbin Johnson Babatunde Kokumo, wanda ya yi ritaya daga aikin a ranar 15 ga Maris ɗin wannan shekara.
The Punch ta ruwaito cewa, daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ne ya bayyana naɗin nasa a matsayin sufeto na riƙon ƙwarya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abubuwa shida da ya kamata ku sani game da sabon sufeton
Ga abubuwa guda shida da ya kamata ku sani game da sabon sufeton 'yan sandan Najeriya na riƙon ƙwarya da aka naɗa:
1. Egbetokun ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Legas, a fannin lissafi a watan Yuni 1987; sannan ya karantar da ilimin lissafi a kwalejin fasaha ta Yaba da ke Legas, kafin shigarsa aikin ɗan sanda.
2. Ya kuma yi digiri na biyu a fannin nazarin fasahohi a jami'ar Legas, sannan ya yi babbar difloma a fannin tattalin arziƙin man fetur a jami’ar jihar Delta, sannan kuma ya yi wani digirin na biyu a bangaren kula da kasuwanci a jami’ar Jihar Legas.
3. Egbetokun ya kasance tsohon kwamishinan ‘yan sanda ne na jihar Legas.
4. A shekarar 1999 aka nada shi babban jami’in tsaro na shugaba Tinubu lokacin yana gwamnan jihar Legas.
5. Ya yi aiki a matsayin Kwamanda, rundunar kawo ɗaukin gaggawa a Legas, kwamandan jami'an 'yan sanda na Mopol a Benin City, jami’in yaki da zamba, a rundunar 'yan sanda na Abuja.
6. Haka nan ya kuma riƙe kwamandan yankin Osogbo, jihar Osun, da kwamandan yankin Gusau, jihar Zamfara da dai sauransu.
Tinubu ya sallami hafsoshin tsaro na ƙasa
A baya, Legit.ng ta kawo muku labarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da dakatar da duk hafsoshin tsaron Najeriya, tare da babban sufeton 'yan sanda na ƙasa.
Sanarwar dakatarwar ta fito ne ta ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya na ƙasa, wacce Willie Bassey, jami'in yaɗa labaran ofishin ya sanyawa hannu.
Asali: Legit.ng