Shugaba Tinubu Ya Sallami Baki Ɗaya Hafsoshin Tsaron Najeriya Da IGP

Shugaba Tinubu Ya Sallami Baki Ɗaya Hafsoshin Tsaron Najeriya Da IGP

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa baki ɗaya hafsoshin tsaro da IGP na ƙasa ritaya daga ranar Litinin, 19 ga watan Yuni
  • Wannan na kunshe a wata sanarwa da Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya fitar, ya kuma naɗa sabbin waɗanda zasu maye gurbinsu
  • Haka zalika Tinubu ya ɗaga matsayin Malam Nuhu Ribadu zuwa mai ba sha shawara kan tsaron ƙasa (NSA)

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sallami baki ɗaya hafsoshin tsaron Najeriya da Sufeta janar na yan sanda daga bakin aiki.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa shugaban kasan ya kuma ƙara ɗaga matsayin Malam Nuhu Ribaɗu zuwa matsayin mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa (NSA).

Hafsoshin tsaron Najeriya.
Shugaba Tinubu Ya Sallami Baki Ɗaya Hafsoshin Tsaron Najeriya Da IGP Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Ma'aikacin INEC Har Lahira, Sun Sace Matarsa

Jaridar Punch ta rahoto cewa sauran waɗanda Tinubu ya sallama daga aiki sun haɗa da, masu ba da shawara ta musamman da ya gada da shugaban hukumar kwastam ta ƙasa, Hamid Ali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani sashin sanarwan mai ɗauke da sa hannun Sakataren gwamnati, George Akume, ta ce:

"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da yi wa baki ɗaya hafsoshin tsaro, sufetan yan sanda na kasa, masu bada shawara da kwanturolan kwastam ritaya nan take."

A ruwayar jaridar Vanguard, shugaban ƙasan ya sanar da sunayen waɗanda zasu maye gurbinsu kuma matakin zai kama aiki nan take.

Jerin shugabannin hukumomin tsaron da Tinubu ya yi wa ritaya daga aiki

Shugabannin tsaron da Tinubu ya sallama daga aiki sun kunshi, babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor, shugaban hukumar sojin kasa, Farouk Yahaya, da shugaban hukumar sojin ruwa, Awwal Gambo.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: A Karshe, Tinubu Ya Gana Da Dangote, Bill Gates A Abuja, Ya Bayyana Inda Zaifi Bai Wa Fifiko

Sauran sun haɗa da shugaban hukumar sojin saman Najeriya, Isiaka Amao da Sufeta janar na rundunar yan sanda ta ƙasa, IGP Usman Alƙali Baba.

FG Ta Koma Teburin Tattauna da NLC, TUC Kan Cire Tallafin Man Fetur

A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin shugaba Tinubu ta sake komawa teburin tattaunawa da wakilan kungiyoyin kwadugo kan batun cire tallafin man fetur.

Taron yau Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023 ya gudana a ɗakin taro na ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262