A Karshe, Tinubu Ya Gana Da Dangote, Bill Gates A Abuja, Ya Bayyana Inda Zaifi Bai Wa Fifiko

A Karshe, Tinubu Ya Gana Da Dangote, Bill Gates A Abuja, Ya Bayyana Inda Zaifi Bai Wa Fifiko

  • Attajiran musu kudi a duniya, Aliko Dangote da Bill Gates sun kai ziyara fadar shugaban kasa, Bola Tinubu a yau Litinin
  • Dangote ya ce ziyarar sun kai ta ne don sanarwa shugaban irin ayyukan Gidauniyar Dangote da kuma Gidauniyar Melinda da Bill Gates
  • A ranar Juma'a 16 ga watan Yuni ne Aliko Dangote ya kai ziyara wurin Tinubu tare da sanar masa zuwansu da Bill Gates

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya gana da shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote da shahararren mai kudin duniya, Bill Gates a fadarsa da ke Abuja.

Ziyarar Bill Gates ba ta rasa nasaba da neman hadin kan shugabanni don kawo ci gaba a Nahiyar Afirka.

Tinubu ya gana da Dangote da Bill Gates
Tinubu Ya Gana Da Dangote Da Bill Gates A Abuja. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

TheCable ta tattaro cewa a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni, Dangote ya gana da shugaban kasa Tinubu a fadarsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sallami Hafsoshin Tsaro da IGP Daga Aiki, Ya Naɗa Sabbin Da Zasu Maye Gurbinsu

Gidauniyar Gates ta ce a yayin ziyarar, attajirin zai gana da shugabannin kasa da kuma na yankuna don kara musu kwarin gwiwar zuba hannun jari da zai inganta ci gaba duk da matsalar tattalin arziki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya yabawa hadin kan Bill Gates da Dangote

A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin bai wa bangaren lafiya fifiko da kuma kare lafiyar 'yan Najeriya.

Bayan yabawa Bill Gates da ya yi, duba da irin ci gaba da yake bayarwa ga al'umma, Tinubu ya yabi hadin kai da ke tsakanin attajiran guda biyu.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yiyuwa don ganin Najeriya da Nahiyar Afirka ta ci gaba musamman ta bangaren kare cututtuka a yankin.

Yayin da yake amsa tambayoyi bayan ganawar, Dangote ya taya Shugaba Bola Tinubu samun nasara da kuma karbar rantsuwar kama aiki, cewar BusinessDay.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Ma'aikacin INEC Har Lahira, Sun Sace Matarsa

Dangote ya fadi dalilin kai ziyarar

Ya ce musabbabin ziyarar shi ne sanarwa shugaban ayyukan da Gidauniyar Melinda da Bill Gates da kuma Gidauniyar Aliko Dangote suke yi.

Dangote ya yabawa Tinubu kan cire tallafin man fetur, inda ya ce hakan zai kawo kudaden da za a saka su cikin harkan lafiya da ilimi da tattalin arziki.

Dangote, Bill Gates Za Su Gana Da Tinubu A Ranar Litinin A Fadar Shugaban Kasa

A wani labarin, shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote da Bill Gates za su gana da Shugaba Tinubu a ranar Litinin 19 ga watan Yuni.

Dangote shi ya bayyana haka yayin ganawar sirri da shugaban kasar a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni.

Ana sa ran ziyarar ba za ta rasa nasaba da ayyukan Gidauniyar Melinda da Bill Gates da kuma ta Aliko Dangote ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.