Anambra: Yan Bindiga Sun Sheka Barzahu Yayin da Suka Kai Wa Jami'an Tsaro Hari

Anambra: Yan Bindiga Sun Sheka Barzahu Yayin da Suka Kai Wa Jami'an Tsaro Hari

  • Wasu 'yan bindiga 15 sun kwashi kashinsu a hannun dakarun 'yan banga a yankin ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra
  • Rahoto ya nuna cewa 'yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan bangan da tunanin suna bacci da safiyar Litinin, 19 ga watan Yuni
  • Kakakin hukumar yan sandan Anambra ya ce yayin musayar wuta 'yan banga suka halaka 'yan bindiga biyu kuma suka kwato makamai

Anambra - Dakarun ƙungiyar 'yan banga sun halaka 'yan bindiga biyu a kauyen Ojika, ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun gamu da ajalinsu ne a hannun mambobin tawagar 'yan bangan Anambra (AVG) da safiyar yau Litinin.

Harin yan bindiga a jihar Anambra.
Anambra: Yan Bindiga Sun Sheka Barzahu Yayin da Suka Kai wa Jami'an Tsaro Hari Hoto: dailytrust
Asali: Depositphotos

Rahoton Punch ya tattaro cewa maharan, waɗanda suka kai mutum 15, sun kutsa kai cikin sansanin 'yan Bangan, a tunaninsu duk suna kwance suna bacci.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Yi Ta’adi Cikin Dare a Kaduna, Sun Harbe Basarake Da ‘Ya ‘Yansa 4

Ɗaya daga cikin mambobin kungiyar 'yan bangan ya shaida wa yan jarida bisa sharaɗin boye sunansa cewa 'yan bindiga sun kai musu harin ɗauke da bindigun AK-47 da layu a jikinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, maharan sun ɗaura layu a wuya, ƙugu, hannu da kafafunsu a sa'ilin da suka shiga sansaninsu. A kalamansa ya ce:

"Suna shigowa suka buɗe mana wuta ba su san cewa kuka suka kawo gidan mutuwa ba. Su ci gaba da zuwa mun shirya tarbansu, marasa hankali kawai."

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abinda ya faru

A halin yanzu, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin da safe.

DSP Tochukwu ya ce, "Eh tabbas, yan bindiga guda biyu sun gamu da ajalinsu a yankin ƙaramar hukumar Ihiala."

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojin Sama Sun Soye Kwamandojin ISWAP a Wani Hari Kan Maboyarsu a Jihar Borno

A cewarsa, 'yan bindigan sun yi yunkurin kai farmaki kan yan bangan Ihiala, amma suka daƙile mummunan nufinsu, kuma suka kashe 'yan bindiga biyu a musayar wuta.

Ya kuma ƙara da cewa an kwato bindigun AK-47 guda biyu da wasu manyan makamai masu haɗari daga hannun maharan.

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Coci a Jihar Benuwai

A wani rahoton na daban Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da babban Malami Coci a jihar Benuwai.

Wani ganau mai suna Oche, ya shaida cewa maharan sun shiga garin da karfe 10:00 na daren ranar Alhamis, suka wuce kai tsaye zuwa harabar Coci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262