Rudani Yayin da Zoben Daurin Aure Ya Ki Shiga Yatsan Ango, Bidiyon Ya Girgiza Intanet
- An sha kallo a lokacin da ake bikin daurin auren wani mutum da amaryarsa a yanayi mai daukar hankali
- Sulut Soja a kafar TikTok, ya yada wani gajeren bidiyo da ke nuna yadda zoben angon ya ki shiga yatsansa
- Zoben da aka kawo wa amarya da angon a wurin daurin auren ya yi kankanta ga babban yatsan angon, lamarin da ya jawo cece-kuce
Bidiyon bikin daurin aure mai ban mamaki na amarya da ango mai ban dariya ya haifar da martani a kafar TikTok.
An yi dirama a lokacin da mutane suka taru don shaida daurin auren sai kawai zoben ango a ki shiga yatsarsa.
An ga hakan ne a cikin wani bidiyon da Sulut Soja ya yada a kafar TikTok, lamarin da ya ja hankali.
Bidiyo ya nuna lokacin da zoben ango ya ki shiga yatsarsa
Da alama zoben daurin auren ya yi kankanta ga yatsarsa ne wanda ke nuna kamar ba a gwada ba kafin halartar wurin bikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan shan faman saka zoben cikin yatsar angonta, sai kawai amaryar ta fusata ta fizge daga hannun angon.
Haka dai wasu mutane a wurin bikin suka yi kokarin taya su soka zoben, amma kokarinsu ya ci tura.
Daga karshe dai aka hakura, aka bar batun zobe a rabi-da-rabi har aka daura auren tunda an gama shiri.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a a kafar sada zumunta
Bayan ganin bidiyon, mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali, inda suka fadi ra’ayoyinsu game da auren ango da amaryar. Ga shi kamar haka:
@nandutu Agnes proud gishu:
"Amma kamar amaryar ba fara’a a fuskarta."
@Bongie Medium:
"Ko ki aure ni yau ko kuma ba za mu yi aure ba har abada. Auren gaggawa. Ina bukatar irin wannan cikin gaggawa.”
@ollybolly777:
"Wayyo Allah ban taba ganin rigar aure irin wannan ba.”
@bessykendimugambi:
"Wannan gaske ne ko wasan kwaikwayo?”
Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2
Yayin da ake kan ganiyar daura aurensu, ango ya fusata, ya bayyana janyewa daga takarar shiga zuciyar amarya.
Wannan lamari ya dauki hankali, inda mutane da yawa suka bayyana martaninsu mai daukar hankali a kai.
Angon ya gano cewa, budurwar da zai aura ta taba haihuwa har sau biyu, don haka ya hakura da batun auren.
Asali: Legit.ng