Hukumar NDLEA Ta Yi Ram da Wasu Rikakkun Masu Safarar Miyagun Kwayoyi a Birnin Legas

Hukumar NDLEA Ta Yi Ram da Wasu Rikakkun Masu Safarar Miyagun Kwayoyi a Birnin Legas

  • Hukumar NDLEA ta yi nasarar kame wasu kasurguman masu safarar miyagun kwayoyi a jihar Legas
  • An bankado cewa, suna harkallarsu ne a kasashen Najeriya da Qatar kafin dubunsu ta cika a watan Yuni
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin da kuma daukar matakin doka da ya dace

FCT, Abuja - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wasu rikakkun masu safarar miyagun kwayoyi biyu 'yan Najeriya da ke zaune kasar Qatar.

Sun shiga hannu ne biyo bayan kama kayansu mai dauke da haramtattun magungunan methamphetamine a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke birnin Ikeja a jihar Legas.

Daraktan yada labarai na hukumar, Mista Femi Babafemi ya bayyana a Abuja ranar Lahadi cewa wadanda aka kaman sune Eyah Nnamdi, wanda aka fi sani da Murphy da Ugwuoke Oluchukwu.

Kara karanta wannan

DSS Ta Gano Makuden Kudade A Gidan Emefiele? Gaskiya Ta Bayyana

Yadda aka kama masu safarar kwaya
Wadanda aka kama da kayayyakin da aka kama | Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Yadda aka kama mutumin farko

Ya bayyana cewa, Oluchukwu ne na farko da aka kama a ranar 9 ga watan Yuni yayin da ake sauke fasinjojin jirgin Qatar Airways a filin jirgin saman na Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa jami’an NDLEA sun kama Oluchukwu da ke shirin tafiya birnin Doha da fasfo din kasar Ivory Coast da sunan Hien Narcisse.

Babafemi ya ci gaba da cewa, binciken da aka yi a jakarsa ta sa aka gano ya boye fakiti biyu na sinadarin methamphetamine ma nauyin kilo 1.

Dalla-dalla: Yadda NDLEA ta yi aikinta

A kalamansa:

“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin dan Najeriya ne da ya samu fasfo din Ivory Coast domin tafiye-tafiyensa.
“Ya furta cewa ya shiga Qatar a watan Agustan 2022 kuma ya dawo Najeriya a watan Afrilun 2023 don kammala shirye-shiryen jigilar kwayoyin.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

“Bincike ya kai ga fallasa wani babban abokin harkallar Oluchukwu mazaunin Qatar da ke wannan sana’ar wanda aka bayyana sunansa da Murphy wanda ke labe a Eziani, mahaifarsa a karamar hukumar Nsukka ta jihar Enugu.
“Oluchukwu wanda ya fito daga karamar hukumar Igboeze ta Arewa ya yi ikirarin cewa yana da kwalin difloma a fannin Injiniyancin Lantarki.
“Tura jami’an NDLEA cikin gaggawa zuwa yankin Eziani a ranar 10 ga watan Yuni ya kai ga kama ‘Murphy’.
"Daga baya an gano ainihin bayanansa cewa sunansa Eyah Celestine Nnamdi, wanda ya zauna a Indonesia na wasu shekaru kafin ya koma Doha."

Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

A wani labarin, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kame wani matashi mai shekaru 34 a Kudancin Amurka daga yankin Suriname mai suna Dadda Lorenzo Harvy Albert.

Daraktan NDELA kan yada labarai, Mr Femi Babafemi ne ya bayyana kamun a ranar Lahadi 9 Afirilu, 2023 a babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Aika Yan Ta'adda 42 Lahira, Sun Cafke Wasu 96 A Arewacin Najeriya

Babafemi ya ce, an kama mutumin ne a filin saukan jirage na Fatakwal a jihar Ribas a lokacin da ya shigo Najeriya da daurin hodar iblis 117.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.