Miyagun Mahara Sun Halaka Basaraken Fulani Da Iyalansa a Zaria

Miyagun Mahara Sun Halaka Basaraken Fulani Da Iyalansa a Zaria

  • Wasu mahara sun kai wani mummunan hari a wani ƙauyen Fulani cikin ƙaramar hukumar Zaria ta jihar Kaduna
  • Maharan sun halaka babban basaraken ƙauyen (Ardo) tare da ƴaƴansa guda huɗu waɗanda duk magidanta ne masu aure
  • Maharan sun kuma yi awon gaba da shanun basaraken waɗanda yawansu ya wuce guda 100 bayan sun halaka shi

Jihar Kaduna - Miyagun mahara sun kai wani mummunan farmaki a gidan Ardon Birni da kewayen Zaria, Alhaji Shuaibu Mohammed, a daren ranar Asabar.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa a yayin harin, maharan sun halaka Alhaji Shuaibu Mohammed tare da ƴaƴansa guda huɗu.

Mahara sun halaka babban basaraken Fulani a Zaria
Gawarwakin Ardon da yayansa Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

Maharan dai su biyar ne suka kawo hari a ƙauyen Dorayi cikin ƙaramar hukumar Zaria, inda suka shiga gidan basakaren suka aikata wannan ta'asar.

Matar marigayin Mallama Halima Shu’aibu ta bayyana cewa maharan sun dirar musu cikin gida ne da misali ƙarfe 10:00 na daren ranar Asabar, inda suka wuce ɗakin Ardon sannan suka halaka shi, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojin Sama Sun Soye Kwamandojin ISWAP a Wani Hari Kan Maboyarsu a Jihar Borno

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan sun halaka basaraken, maharan sun riƙa shiga ɗaki-ɗaki na ƴaƴansa guda huɗu waɗanda duk magidanta ne sannan suka kashe su.

Malama Halima ta bayyana sunan ƴaƴan da suka rasa rayukansu a harin da suma haɗa da Haruna Shuaibu, Musa Shuaibu, Adamu Shuaibu da Abubakar Shuaibu.

Maharan sun kora musu shanu

Malama Halima ta ci gaba da cewa bayan maharan sun kammala kisan, sai kuma suka kora musu shanu waɗanda yawansu ya kai guda 100.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan Ardon wanda ya tsira da ransa, Abdurrahman Shuaibu, ya bayyana cewaa bayan ɓata-garin sun kammala cin karensu babu babbaka a gidansu, sun kuma harbi wasu mutum biyu a hanyarsu ta ficewa daga ƙauyen.

Ko da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce zai tuntubi babban jami’in ƴan sanda na Zaria don jin cikakken bayani kan yadda lamarin ya auku

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Halaka Bayin Allah Suna Cikin Noma A Gonakinsu A Kaduna A Wani Sabon Hari

Sai dai, ba a sake jin ɗuriyar kakakin ba har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma a Kaduna

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna, inda suka halaka wasu manoma.

Ƴan bindigan dai sun ritsa da manoman ne suka tsaka da aiki a gonarsu onda suka halakasu ba gaira babu dalili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng