Cikakkun Sunaye: Majalisar NJC Ta Ba Da Shawarar Nada Ma'aikatan Shari’a 37 a Kotuna Daban-Daban

Cikakkun Sunaye: Majalisar NJC Ta Ba Da Shawarar Nada Ma'aikatan Shari’a 37 a Kotuna Daban-Daban

  • Majalisar shari'a ta kasa (NJC) ta gudanar da taronta na 102 a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, da Alhamis, 15 ga watan Yuni
  • Babban Alkalin alkalan Najeriya, Justis Olukayode Ariwoola, ne ya jagoranci taron
  • Majalisar NJC na duba rahoton kwamitinta sannan ta ba da shawarar nada ma'aikatan shari'a 37 a mukamai daban-daban

FCT, Abuja - Majalisar harkokin shari’a a Najeriya (NJC) ta bayar da shawarar nada mutane tara a kotun daukaka kara.

Hakazalika ta bayar da shawarar nada wasu ma'aikatan shari'a 27 a kan wasu mukamai, jaridar Punch ta rahoto.

Shugaban alkalan Najetiya
Cikakkun Sunaye: Majalisar NJC Ta Ba Da Shawarar Nada Jami’an Shari’a 37 a Kotuna Daban-Daban Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Majalisar NJC ta bayar da shawarar nada mutane da dama a matsayin alkalan kotun daukaka kara

A wata sanarwa da ta saki a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni, majalisar ta bayyana cewa ta ba da sabbin shawarwarin ne a taronta na 102, wanda ya gudana tsakanin Laraba, 14 ga watan Yuni da Alhamis, 15 ga watan Yuni, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rai da ajali: Hawaye sun kwaranya yayin da fitaccen basaraken da ya fi dadewa a jiha ya kwanta dama

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da daraktar yada labaran majalisar, Soji Oye, ya saki.

Ya kuma ce taron karkashin jagorancin shugaban alkalan Najeriya kuma shugaban NJC, Olukayode Ariwoola, ta yanke shawarar ne bayan duba rahoton da kwamitin daukan aikinta ya gabatar.

Rahoton na dauke da sunayen mutane 37 da aka bayar da shawarar nada su a mukaman shari'a daban-daban.

An mika sunayen mutane tara wadanda za su yi aiki a kotun daukaka kara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu don tabbatar da su.

Duba cikakkun jerin sunayen mutane 37 din a kasa:

  • Alkalai 9 na kotun daukaka kara
  1. Justis Jane Esienanwan Inyang
  2. Justis Paul Ahmed Bassi
  3. Justice Lateef Adebayo Ganiyu
  4. Justice Hadiza Rabiu Shagari
  5. Justice Okon Efreti Abang
  6. Justice Asma’u Musa Mainoma
  7. Justice Hannatu Azumi Laja-Balogun
  8. Justice Binta Fatima Zubair
  9. Justice Peter Chudi Obiora

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

  • Alkalai 3 Judges na babbar kotun jihar Benue
  1. Lilian Ngusuur Terseer-Tsumba
  2. Patrick Eka Oche
  3. Ukande Mvendaga Peter
  • Alkalai 8 na babbar kotun jihar Edo
  1. Ovenseri Otamere
  2. Obayuwana Osarenren Mathias
  3. Edoghogho Eboigbe
  4. Ojo Maureen Osa
  5. Bright Eraze Oniha
  6. Ehinon Anthony Okoh
  7. Godwin Jeff Okundamiya
  8. Osayande Ikwuemosi Awawu
  • Alkalai 5 na babbar kotun jihar Delta
  1. Ossai Rita Ngozi
  2. Aforkeya Obomejero
  3. Adolor Sunny Onorieukuhakpo
  4. Samuel Ifeanyi Okeleke
  5. Umuko Aboyowa Godwin
  • Babban Alkali na babbar kotun jihar Bayelsa

Justis Matilda Abrakasa Ayemieye

  • Babban Alkali na babbar kotun jihar Edo

Justis Daniel Iyobosa Okungbowa

  • Babbar Alkali na babbar kotun jihar Kano

Justis Dije Abdu Aboki

  • Alkalin kotun daukaka kara na jihar Benue

Lortyer Vihilun Fidelis

  • Shugaban kotun daukaka kara na jihar Delta

Justis Catherine Ngozi Ojugbana-Orishedere

  • Alkalai 4 na babbae kotun jihar Katsina
  1. Nurudeen Abdulmumeen
  2. Halima Lawal Bagiwa
  3. Abdullahi Bara’u Faskari
  4. Sanusi Ma’aruf Aminu

Kara karanta wannan

Daga Ribadu Zuwa Olukoyede: Jerin Sunayen Shugabannin EFCC Da Jihohi/Yankunansu

  • Alkalin kotun daukaka kara na jihar Delta

Sofowora Oriyomi Abiodun

  • Alkalai 2 na kotun daukaka kara na jihar Benue
  1. Gbakeji Michael Emakpor
  2. Uraih Tracy Patricia Ifeanyi

“Muna Bukatar EFCC Da Za Ta Nuna Kwazo a Aiki”: An Yaba Ma Tinubu Kan Dakatar Da Bawa

A wani labari na daban, Babajide Otitoju, shararren dan jarida, ya bayyana cewa mutuwar Abba Kyari ne sanadin samun sauyi a shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Da yake magana kan dakatar da Abdulrasheed Bawa, tsohon shugaban EFCC a tashar TVC news kamar yadda Ayekooto ya wallafa a Twitter, shahararren dan jaridan ya ce da ace Kyari na raye, da Bawa ba zai zama shugaban hukumar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel