“Muna Bukatar EFCC Da Za Ta Nuna Kwazo a Aiki”: An Yaba Ma Tinubu Kan Dakatar Da Bawa

“Muna Bukatar EFCC Da Za Ta Nuna Kwazo a Aiki”: An Yaba Ma Tinubu Kan Dakatar Da Bawa

  • An zargi Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban EFCC da nuna son kai wajen hukunta masu laifi
  • Shahararren dan jarida, Babajide Otitoju, ne ya yi zargin yayin da yake kare matakin da Tinubu ya dauka na dakatar da shugaban EFCC
  • Otitoju ya ce mutuwar Abba Kyari, COS na tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi yasa aka cire Ibrahim Magu cikin sauki

Babajide Otitoju, shararren dan jarida, ya bayyana cewa mutuwar Abba Kyari, marigayi shugaban ma'aikatan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, shine sanadin samun sauyi a shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Da yake magana kan dakatar da Abdulrasheed Bawa, tsohon shugaban EFCC a tashar TVC news kamar yadda Ayekooto ya wallafa a Twitter, shahararren dan jaridan ya ce da ace Kyari na raye, da Bawa ba zai zama shugaban hukumar ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shin EFCC Ta Ayyana Neman Matawalle Ruwa A Jallo? Gaskiya Ta Fito

Bawa, Buhari da Magu
“Muna Bukatar EFCC Mai Kwazo”: An Yaba Ma Tinubu Kan Dakatar Da Bawa Femi Adeshina
Asali: Twitter

Yadda Malami ya kawo Bawa domin ya maye gurnin Magu a matsayin shugaban EFCC

Otitoju ya ce mutuwar Kyari ne ya kulle kofar haduwa da Buhari kan Ibrahim Magu, shugaban EFCC kafin zuwa Bawa, kuma Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a shine ya yi aiki don ganin Magu ya bar ofis.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce bayan tsige Magu daga ofis, Malami ne ya zabi Bawa domin ya zama shugaban EFCC.

A cewar Otitoju, Bawa ya dauke kai daga hukunta yan siyasa a sansanin Malami sannan ya fi mayar da hankali sosai a kan yan damfara da aka fi sani da yan Yahoo-Yahoo maimakon yan siyasa.

An yaba ma Tinubu kan dakatar da Bawa

Ya bayyana dakatar da Bawa a matsayin ci gaba mai kyau sannan cewa kasar na bukatar hukumar yaki da rashawa da za ta yi aiki tukuru.

Kara karanta wannan

Zance ya fito: Bayan Ganawar Tinubu Da Dangote Da Matawalle, Batutuwa Sun Fito Waje

Ku tuna cewa shugaban kasa Tinubu ya dakatar da Bawa a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni kimanin mako guda bayan ya dakatar da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.

Daga Bawa har Emefiele sun amsa tambayoyi daga hukumar tsaro na farin kaya (DSS).

Kalli bidiyon a kasa:

Tattalin arziki da wasu bangarori 3 da Tinubu ya kwankwasa cikin makonsa na 3 a matsayin shugaban kasa

Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya ci gaba da ba yan Najeriya mamaki tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu.

Da ake duba ayyukan shugaban kasar cikin makonsa na uku a matsayin shugaban kasar Najeriya, Tinubu ya aiwatar da manyan manufofi da matakan da suka sauya abubuwa a bangarori daban-daban na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng