'Yan Sanda Sun Mayar Da Motocin Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle Da Suka Kwace

'Yan Sanda Sun Mayar Da Motocin Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle Da Suka Kwace

  • Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta mayar wa da tsohon gwamnan jihar motocinsa da ta ƙwace a gidajensa
  • Ƴan sandan sun mayar wa da Bello Matawalle ne da motocin bayan wata babbar kotun tarayya ta tilasta su yin hakan
  • Matawalle dai ya garzaya kotu bayan da jami'an suka yi wa gidajensa biyu kutse inda suka ƙwace masa motoci da dama

Jihar Zamfara - Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara a ranar Asabar, ta bayyana cewa ta dawo da dukkanin motocin da ta ƙwace daga wajen tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa kakakin rundunar, ASP Yazid Abubakar, shine ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) hakan a wayar tarho ranar Asabar.

'Yan sanda sun mayar da motocin Bello Matawalle
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle Hoto: Bbchausa.com
Asali: UGC

Abubakar ya ce an mayar da motocin ne domin bin umarnin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Kotun wacce mai shari'a Aminu Bappah-Aliyu, ke jagoranta a ranar 15 ga watan Yuni, ta bayar da umarni ga dukkanin hukumomin tsaron da suka ɗauko motoci a gidajen Matawalle na Gudau da Maradun da su mayar da su cikin sa'o'i 48.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaron dai sun ɗauko motocin ne daga gidajen guda biyu bisa umarnin gwamnatin jihar.

Ƴan sanda sun mayar da motocin bayan umarnin kotu

Abubakar ya tabbatar da cewa babu sauran mota ko guda ɗaya ta tsohon gwamnann a hannunsu domin duk sun mayar da su.

A kalamansa:

"Eh tabbas, rundunar ƴan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkanin motocin tsohon gwamna Bello Matawalle."
"Mun mayar da dukkanon motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya a Gusau. A yanzu da na ke maganar nan, babu mota ko guda ɗaya a hannun ƴan sanda."

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: Gwamnan Arewa Ya Samo Mafita, Za a Fara Jigilar Dalibai a Jiharsa Kyauta Ba Ko Kobo

Kotun ta kuma bayar da umarnin hana waɗanda ake ƙara a cikin da Matawalle ya shigar daga ɗaukar wani mataki dangane da lamarin, cewar rahoton Premium Times.

Waɗanda ake ƙarar dai sun haɗa sa babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, rundunar ƴan sanda da kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara.

Sauran sun haɗa da rundunar ƴan sandan fararen kaya (DSS) da hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC).

Matawalle Ƴa Yi Zargin An Masa Sata

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun tattara masa kayayyakin gidajensa lokacin da suka je kwaso motoco a gidansa.

Matawalle ya bayyana cewa hatta hijaban matansa da sauran kayayyaki basu tsira ba inda jami'an tsaron suka yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng