Sarkin Musulmi Ya Ce Musluman Najeriya Su Duba Jinjirin Watan Dhul-Hijjah a Ranar Lahadi

Sarkin Musulmi Ya Ce Musluman Najeriya Su Duba Jinjirin Watan Dhul-Hijjah a Ranar Lahadi

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci Musulman Najeriya da su fara duba jinjirin watan Dhul-Hijjah daga ranar Lahadi
  • Sultan na Sokoto ya ce Lahadi, 18 ga watan Yuni ne 29 ga watan Dhul-Qadah wanda zai zama rana ta karshe da za a nemi jinjirin watan babban sallah
  • Ya kuma roki Allah ya taimaki daukacin al'ummar Musulmi wajen sauke hakokin addini da ya rataya a wuyansu

Sokoto - Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci Musulman kasar da su fara duban jinjirin watan Dhul-Hijjah da yammacin ranar Lahadi

Abubakar ya bayar da umurnin ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bayar da shawarwari kan harkokin addini na masarautar Sokoto, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Ba Mazauna Garuruwa Makamai Domin Yakar ‘Yan Bindiga a Arewa

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi Ya Ce Musluman Najeriya Su Duba Jinjirin Watan Dhul-Hijjah a Ranar Lahadi Hoto: Punch
Asali: UGC

Lahadi ce ranar karshe da za a nemi jinjirin watan Dhul-Hijjah

Dhul-Hijjah ya kasance na 12 kuma na karshe a kalandar Musulunci wanda a cikinsa ne Musulmai ke sauke farali wato aikin Hajji da kuma bikin babban sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta nakalto sanarwar na cewa

"Wannan don sanar da Al'ummar Musulmi ne cewa, Lahadi 18 ga watan Yuni wanda yake daidai da ranar 29 ga watan Dhul-Qadah shine zai zama rana ta karshe da za a nemi jinjirin watan Dhul-Hijjah 1444 AH.
"Don haka ana umurtan Musulmai da su fara neman jinjirin wata a ranar Lahadi sannan su kai rahoton abun da suka gani ga hakimi kauye mafi kusa domin sanar da sarkin Musulmin."

Sanarwar ta kuma roki Allah ya taimaki daukacin al'ummar Musulmi wajen sauke hakokin da ya rataya a wuyansu na addini.

Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addini a jihar Ondo

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Gwamna Lawal Ya Fara Ɗaukar Matakan Kawo Karshen Yan Bindiga a Zamfara

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da da babban limamin masallacin Uso da ke karamar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade.

An tattaro cewa yan bindigar da yawansu ya kai biyar sun sace malamin addinin mai shekaru 67 a gonarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng