Ba Gaskiya Bane: Binciken Gaskiya Ya Tabbatar da Ba a Samu Wasu Kudade a Gidan Godwin Emefiele Ba

Ba Gaskiya Bane: Binciken Gaskiya Ya Tabbatar da Ba a Samu Wasu Kudade a Gidan Godwin Emefiele Ba

  • Rundunar ‘yan sandan sirri ta Najeriya ta kama gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele
  • Kwanaki kadan, wani faifan bidiyo ya rika yawo a wasu kafafen sada zumunta, ciki har da WhatsApp, inda ake cewa an samu kudi a gidan Emefiele
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, 2023, biyo bayan binciken da ake yi a ofishinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 27 wanda ya yadu a kafar sada zumunta ya nuna wasu mutane biyu suna shirya makudan kudade suna kirga su da inji.

Wadanda suka yada bidiyon sun yi nuni da cewa, hukumar DSS ce ta gano wasu makudan kudade a gidan Godwin Emefiele, korarren gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Ba gaskiya bane, ba a gano kudi a gidan Emefiele ba
Bidiyon abin da ake alakanta Emefiele dashi | Hoto: @akerele_s, @cenbank
Asali: Twitter

Tsohon bidiyo ne, kuma daga Sudan

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotu Ta Umurci DSS Ta Saki Emefiele A Cikin Mako 1, Ta Bayyana Dalillai

Legit.ng ta lura cewa galibin wadanda ke yawo da bidiyon magoya bayan shugaba Bola Tinubu ne - kamar yadda ya bayyana a nan da kuma nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakanan, bidiyon wanda ke nuna alamar kudaden dalar Amurka ba shi da sauti.

Jaridar The Cable a cikin bincikenta da ta buga a ranar Juma’a, 16 ga Yuni, ta ce faifan bidiyon ya samo asali ne daga kasar Sudan, wata kasa a Arewacin Afirka.

Bin diddigi ya ce, an sake bidiyon ne a ranar 22 ga Afrilu, 2019, lokacin da aka gano wani babban tafkin kudi - wanda ya kai dalar Amurka miliyan 7 - a gidan Omar Bashir, hambararren shugaban kasar Sudan, inji rahoton Arab News.

A halin yanzu, Bashir yana Asibitin Aliyaa, Omdurman, bayan fitowa daga gidan yari a wani kazamin fada da aka gwabza a kasar.

Kara karanta wannan

'Baba Buhari': Bidiyon Yadda Wasu Yan Najeriya Suka Cika Da Murna Bayan Yin Ido Hudu Da Tsohon Shugaban Kasa Buhari Yana Tafiya a Titin Daura

Tsohon shugaban dan shekaru 79, wanda ya mulki Sudan tsawon shekaru 30, an hambarar da shi ne a wani boren ‘yan tabare da ya barke a shekarar 2019.

DSS ta yi tsokaci game da bidiyon

Hakazalika, Peter Afunaya, mai magana da yawun hukumar DSS, ya bayyana cewa faifan bidiyon da ake alakantawa da Emefiele “karya ne”.

Ya bayyana hakan ne a wata fusatacciyar sanarwar martani ga bukatar da aka yi ya ba da bayani game da bidiyon.

Yanzu dai ana bincike kan Emefiele, kuma ana ganin kamar akwai matsalolin kudi da suka shafi kujerar da ya bari.

Hukumar DSS ta tabbatar da kama Emefiele bayan an musunta hakan da farko

A bangare guda, kunji yadda hukumar DSS ta bayyana kama tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele tare da bayyana halin da yake ciki.

Hukumar ta bayyana kama shi ne, duk da a baya ta ce bata kama shi ba duk da zarge-zargen da aka bayyana.

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike kan tsohon gwamnan game da abubuwan da suka faru a ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.