Abin Takaici: Farfesa Sonyinka Ya Ce Kowa Ya Lura, Kafofin Sada Zumunta Sun Mayar da bil’Adama Baya

Abin Takaici: Farfesa Sonyinka Ya Ce Kowa Ya Lura, Kafofin Sada Zumunta Sun Mayar da bil’Adama Baya

  • Farfesa Wole Soyinka ya yi bayanai masu zafi game da mummunan tasirin da kafafen sada zumunta ke yi ga al’ummar zamanin nan
  • Ya bayyana cewa kafafen sada zumunta sun zama kayan aikin da jahilai ke amfani dashi wajen yada rashin fahimta da raba kan mutane
  • Farfesan da ya lashe kyautar Nobel a shekara ta 1986 ya bayyana cewa shi dai ba ya amfani da kafofin sada zumunta

Jihar Legas - Shahararren marubucin duniya Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa shi dai bai amfani da kafafen sada zumunta kamar yadda ya nuna damuwa kan illar da suke yi ga ‘yan zamanin nan.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, marubucin mai shekaru 88 a duniya ya ce amfani da gamsuwa da kafofin sada zumunta na tsawon shekaru ya mayar da bil’Adam baya saboda amfani da fasahar ta hanyoyin da basu dace ba.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Bayyana Abun Da Wadanda Suka Kafa Boko Haram Suka Fada Masa Game Da Tushen Ta’addanci

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni, a wajen kaddamar da sabon rubutunsa, “The Putin Files,” a Freedom Park da ke jihar Legas.

Farfesa Soyinka ya soki kafafen sada zumunta
Farfesa Wole Soyinka kenan | Hoto: Ramesh Sharma/The India Today Group
Asali: Getty Images

Yayin da yake bayyana ra’ayinsa kan dandalin sada zumunta da amfani da su, Farfesa Soyinka ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ba na yin Twitter, ba na yin WhatsApp. Na taba gwada WhatsApp amma na daina."

Soyinka na da ra’ayoyi daban-daban

A bangare guda, farfesan ya taba bayyana cewa, shi ba ya kan millar kowane addini, inda yace ba Kirista bane shi, kana ba Musulmi ba kuma ba mai bin addinin gargajiya ba.

Babban marubucin ya ce babu ruwansa da addinin kiristanci, Musulunci ko bautar gumaka wato addinin gargajiya, sannan cewa bai taba ji a ransa akwai bukatar ya bautawa wani ba.

Ya ce shi babu wani abun bauta da yake bautawa kuma yana kallon gumaka a matsayin zahirin gaskiya, don haka, sune abokan tafiyarsa a duk lokacin da yayi balaguro imma a zahiri ko a badini.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

Ba sabon abu bane samun wadanda ke barranta da dukkan addinai ba, hakan na yawan faruwa a duniya.

Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani Bayerabe ne ba Bafulatani ba

A wani labarin, an taba samun lokacin da shanu suka taba kutsawa gidan Farfesa Soyinka a jihar Ogun.

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta sanar da cewa shanun da suka kutsa cikin gidan Wole Soyinka na wani bayerabe ne.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya ce shanun na wani Kazeem Sorinola ne wanda ya dauka wani Bafulatani wanda yake kula da shanun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.