Rusau: Al’ummar Kano Sun Fusata, Suna Zargin Gwamnati da Rashin Bin Ka’idoji Are da Barnata Dukiyoyin Jama’a
- An samu firgici yayin da wasu jami’an gwamnatin Kano suka zo rushe gine-gine a yankin Salanta
- Mazauna yankin sun yi turjiya, sun nuna kin amincewarsu da tsarin gwamnatin Kano mai rushe-rushe
- Tun kafin karbar mulki, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin kwace filayen gwamnatin jihar Kano
Jihar Kano - Mazauna unguwar Salanta Quarters da ke cikin birnin Kano sun zargi gwamnatin jihar da ruguza gine-ginensu ba tare da an sanar dasu ko ba su diyya ba.
Mazaunan wadanda suka bayyana rushe gidajen nasu da cewa ya sabawa doka, sun ce sun bi tsarin da ya dace wajen mallakar filayen daga tsohuwar gwamnati.
An samu firgici da hankali a yankin a ranar Asabar yayin da mazauna yankin suka yi kokarin hana jami'an da aka turo don yin rushe-rushen aiwatar da nufinsu.
Wani faifan bidiyo na inda rikicin ya auku ya nuna yadda wani ya jikkata kana yake kiran waya do neman taimako daga abokansa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jami’an gwamnati sun mana barna
Ya bayyana cewa, a lokacin da jami’an rusau din suka zo, sun lalata daya daga wayoyin hannunsa.
“Ba daidai bane ku rusa gine-ginemu cikin dare ba tare da sanar da mu ba bayan muna da dukkan takardun da ake bukata. Dukanmu da da iyalanmu a nan, kuma wannan zalunci ne. Sun zabo mana bala'i."
Jaridar Premium Times ta kai ziyara inda lamarin ya faru a ranar Asabar don shaida yadda aka barnata gine-ginen jama’ar yankin.
Gwamnati bata yi martani ba
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an tattaro cewa, babu ginin da aka rusa saboda turjiyar jama’ar yankin.
A wurin, an kuma gano wasu gine-ginen da aka rusa, inda kuma wasu ‘yan kwasar ganima ke kokarin kwashe kayan da aka lalata.
Jaridar ta yi kokarin jin ta bakin Sanusi Bature, mai magana da yawun gwamnan, amma hakan ya ci tura.
Alwashin gwamnati kan rushe-rushe a filayen gwamnati
Sai dai, a tsagin gwamnati, ta zargi gine-ginen yankin na Salanta da cewa, an gina su ba bisa ka’ida ba kuma a kan filayen Kwalejin Fasaha ta jihar Kano
A tun farko, sakataren gwamnan jihar, Abdullahi Baffa ya ce gwamnatin Abba Gida-Gida za ta kwato dukkan filaye mallakin gwamnati.
Duk da wannan rushe-rushe, gwamnatin Kano za ta fara tura ‘ya’yan talakawa karatu kasashen waje nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng