Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 2 A Gonakinsu Jihar Ƙaduna
- Ƴan bindiga sun sake kai hari a yankin Birnin Gwari inda suka halaka wasu manoma mutum biyu a gonakinsu
- Ƴan bindigan sun halaka manoman ne a yayin da su ke tsaka da aiki a gonakinsu ranar Juma'a a ƙauyen Unguwar Gajere
- A ranar Alhamis ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu manoman guda biyu a ƙauyen Gwanda mai Gyada
Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun halaka. wasu ƴan uwan juna suna tsaka da noma a ƙauyen Unguwar Gajere, cikin mazaɓar Kutemeshi, a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Juma'a da safe lokacin da mutanen su ke aiki a gonakinsu.
Sagir Umar, wani mazaunin yankin ya nuna damuwarsa kan yadda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin, wanda hakan ya tada hankulan mutanen ƙauyen.
Ƴan bindiga sun addabi yankin da hare-hare
Ya bayyana cewa a cikin sati biyu da suka gabata, aƙalla mutanen ƙauyen mutum 10 ƴan bindiga suka riƙe a hannunsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Umar, ƴan bindigan sun addabi mutanen ƙauyen ta hanyar yi musu ɗauki ɗai-ɗai da sace musu dabbobi.
Yahaya Musa, ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar Kakangi, ya tabbatar da aukuwar kisan na kwanan nan sannan ya nuna takaicinsa kan lamarin.
Ya kuma ƙara bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma sace wasu manoman guda biyu a ƙauyen Gwanda mai Gyada, a ranar Alhamis suna cikin aiki a gonakinsu.
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar domin jin ta bakinsa, DSP Mohammed Jalige, ya yi alƙawarin zai sake kiran wakilin majiyarmu domin bayar da cikakken bayani kan lamarin.
Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba sake jin ɗuriyarsa ba.
'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Malamin Coci a Jihar Benue
A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun sace wani malamin cocin Otukpo Diocese, Rabaran Anthony Adikwu
Malamin Cocin da miyagun suka yi garkuwa da shi yana aiki a cocin St. Margaret’s Parish da ke garin Ajegbe Awume, ƙaramar hukumar Ohimini ta jihar Benue.
Asali: Legit.ng