Obasanjo: Wadanda Suka Kafa Boko Haram Sun Fada Mani Cewa Ainihin Abin Da Ya Haifar Da Ta'addanci
- Olusegun Obasanjo ya bayyana abun da wadanda suka kafa Boko Haram suka ce masa ya haifar da ta'addanci a arewa maso gabas
- Tsohon shugaban kasar ya ce jagororin kungiyar sun ce talauci da rashin aikin yi ne ya tursasa su shiga harkar ta'addanci
- Obasanjo ya yi gargadin cewa idan ba a yi wani abu a kai ba, yara fiye da miliyan 20 da basa makaranta suna iya zama yan Boko Harama a gaba
Lagos - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana abun da wadanda suka kafa kungiyar ta'addancin Boko Haram suka fada masa ya haifar da ta'addanci tun da farko.
Obasanjo ya ce wadanda suka kafa Boko Haram a arewa maso gabas sun fada masa cewa talauci da rashin aikin yi ne ya tursasa su shiga ta'addanci, jaridar Punch ta rahoto.
Dattijon kasar ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi wajen kaddamar da wani littafi mai suna ‘Pillars of Statecraft: Nation-building in a changing world’ wanda diyarsa, Dr. Kofo Obasanjo-Blackshire, ta wallafa a jihar Lagas.
"A farkon fara Boko Haram, lokacin da aka ce an kashe mutumin da ya fara fafutukar, na ce ina so na gana da mambobin kungiyar don tattaunawa da su da kuma sanin abun da suke so.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na hadu da wakilansu sannan na gano cewa basa bukatar komai face ingantaccen rayuwa wa kansu. Shin za mu ga laifinsu don su so wa kansu ingantaccen rayuwa?
"Sun ce sun yarda da Shari'a. Na fada masu cewa Shari'a ba matsala bace a Najeriya. Yana cikin kundin tsarinmu."
Sai dai kuma, Obasanjo ya yi gargadin cewa yawan yara da basa zuwa makaranta na iya kasancewa tayar da yan Boko Haram a gaba.
Ya ce:
"Muna da yara fiye da miliyan 20 da basa zuwa makaranta. Ku duba intanet ku ga kasashe nawa ne ke da kasa da 20m. Wannan baya damun mu? Kuna tunanin za a iya samun Boko Haram a gobe?
"Wadannan sune tushen Boko Haram dinku na gobe. Ya kamata wannan ya dame mu. Kada mu ce daga waje aka shigo da su. Shin talauci daga waje ne? Talauci zabin shuwagabannin mu ne. Idan muka ce a'a; ba zai kasance ba. Idan muka ce eh; zai zama eh."
Yan Boko Haram sun kai hari Borno, sun yi wa mutum 15 yankan rago
A wani labari na daban, mun ji cewa wasu da ake zaton yan ta'addan Boko Haram ne sun yi wa akalla mutane 15 yankan rago a wasu hare-hare da suka kai kan garuruwa biyu a karamar hukumar Jere ta jihar Borno.
Maharan sun farmaki kauyen Kofa da tsakar dare sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi, wanda ya shafe kimanin awa daya zuwa safiyar Juma'a.
Asali: Legit.ng