Shugaba Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Kara Motocin Kashe Gobara a Ayarinsa

Shugaba Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Kara Motocin Kashe Gobara a Ayarinsa

  • Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sanya motocin kashe gobara a cikin ayarin tawagar shugahan ƙasa
  • Shugaban hukumar kwana-kwana na ƙasa ya ce wannan ne karon farko da shugaban ƙasa ya yi haka a tarihin Najeriya
  • Ya ce tuni sabbin kananun motocin kashe gobara da hukumar ta cefano suka iso, a halin yanzu suna jiran kaddamarwa

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kafa tarihi yayin da ya amince da sanya motocin kwana-kwana a cikin ayarin motocin tawagar shugaban ƙasa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wannan matakin da Tinubu ya ɗauka, ya sa ya zama shugaban ƙasa na farko a tarihin Najeriya da motocin kwana-kwana zasu shiga ayarinsa.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Kara Motocin Kasje Gobara a Ayarinsa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Shugaban hukumar kashe gobara ko mu ce hukumar kwana-kwana (FFS) na ƙasa, Injiniya Abdulganiyu Jaji, shi ne ya sanar da haka a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Ɗangote da Tsohon Gwamnan Zamfara a Villa, Ya Yi Jawabi Mai Jan Hankali

Abdulganiyu ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince a sanya motocin kashe gobara a cikin jerin gwanon motocinsa, wannan ne karon farko a tarihin Najeriya."

Shugaban hukumar ya bayyana wannan matakin ne yayin da ya kai ziyara ga babban Sakataren ma'aikatar kula da harkokin cikin gida, Dakta Oluwatoyin Akinlade.

Mun siyo kananan motocin kashe wuta guda 15 - Jaji

Bugu da ƙari, shugaban FFS ya yi bayanin cewa hukumar ta cefano sabbin ƙananan motocin kashe gobara guda 15 domin shiga wurararen da manyan motoci ba zasu iya shiga ba.

Ya ce tuni sabbin motocin, waɗanda aka siyo da nufin daƙile gobara tun a matakin farko, suka iso Najeriya amma suna jiran a kaddamar da su domin fara aiki.

Ya kuma kara tuna wa 'yan Najeriya cewa a kwanakin baya ma'aikatar cikin gida ta kaddamar da buɗe babbar tashar 'yan kwana-kwana ta farko a Kubwa, birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Jerin Muhimman Abubuwa 8 Da Gwamnatinsa Za Ta Mayar Da Hankali A Kai

A cewarsa, akwai wasu manyan tashoshi 12 da ke kan matakan kammala wa a faɗin Najeriya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Lawal Na Zamfara Ya Gana da Shugaban Rundunar Tsaro a Abuja

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi ganawar sirri da babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor, a Abuja.

Gwamnan ya roki karin dakarun soji a jihar Zamfara da kuma goyon baya domin kawo karshen ayyukan 'yan bindigan da suka hana mutane zaman lafiya a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262