Dubun Masu Satar Awaki Ta Cika A Gombe Yayin Da 'Yan Sanda Suka Yi Ram Da Su

Dubun Masu Satar Awaki Ta Cika A Gombe Yayin Da 'Yan Sanda Suka Yi Ram Da Su

  • Rundunar 'yan sanda sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen sace-sacen awaki da ake yi a Gombe
  • Mutanen da ake zargi sukan yi amfani da babur mai ƙafa uku wajen gudanar satar, sannan sai su siyar da awakin domin samun kuɗin kashewa
  • 'Yan sandan sun yi nasarar ƙwato kayayyakin da suka haɗa da babur mai ƙafa uku da akuya ɗaya a matsayin shaida

Gombe - Rundunar ‘yan sanda a jihar Gombe ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna cikin gungun masu satar awaki a unguwar Malam Inna da Wuro Kesa da ke ƙaramar hukumar Gombe, jihar Gombe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mahid Abubakar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Juma’a, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Jefa Kansa Cikin Gagarumar Matsala Don Rubutu Da Ya Yi Kan Kabilar Ibo A Tuwita

'Yan sanda sun cafke masu satar awaki a Gombe
'Yan sandan sun cafke matasa da suka kware a satar awaki a Gombe. Hoto: Peoples Gazette
Asali: UGC

Yadda barayin ke gudanar da satar awakin

Abubakar ya ce waɗanda ake zargin suna amfani da babura masu ƙafa uku wajen satar awakin jama'a, waɗanda suke siyarwa domin samun kuɗi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa, sa a ta kwacewa ɓarayin ne daidai lokacin da jami’an shiyyar Gombe da ke aiki bisa wasu bayanai na sirri, suka dirar musu a maɓoyarsu.

Abubakar ya kuma ƙara da cewa, wadanda ake tuhumar sun amsa laifin na su ba tare da wahal da shari'a ba.

A kalamansa:

“Waɗanda ake zargin Abdulaziz Abubakar mai shekaru 20, Abdullahi Shuaibu da ake kira da ​​Dealer, mai shekaru 25, da Hassan Adamu mai shekaru 18, sun amsa laifin a bisa radin kansu.”
“Har yanzu ana ci gaba da bincike kuma nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci.”

Kara karanta wannan

An Maka Budurwa A Kotu Kan Sama Da Fadi Da Naira Miliyan 4 Da Ƙawarta Ta Ba Ta Ajiya A Abuja

"Abubuwan da aka samu a tare da su sun haɗa da babur mai ƙafa uku da akuya guda ɗaya."

An kama mutane 12 saboda da haɗa baki da masu aikata laifuka

Kakakin ya ce an kuma kama wasu mutane 12 da ake zargi da laifin haɗa baki da miyagu, sata da kuma fashi da makami.

Kakakin ya ce waɗanda ake zargin sun amsa laifukan da suka aikata kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu.

Asari Dokubo ya gargaɗi Tinubu kan sakin Nnamdi Kanu

A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa shahararren tsohon ɗan tada ƙayar baya na yankin Neja-Delta, Alhaji Mujahid Asari Dokubo ya gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa kada ya saki shugaban 'yan a ware na Biafra, Nnamdi Kanu.

Dokubo Asari ya shaidawa Tinubun hakan ne a yayin wata ganawa da suka yi da shi a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng