Kotu Ta Jingine Hukuncin da Ya Tsige Sufeta Janar Na Yan Sanda, Usman Baba
- Babbar Kotun tarayya ta jingine hukuncin da ta yanke a watan Mayu, 2023 na tsige IGP Usman Baba daga kan mukaminsa
- A ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2023, Alkalin Kotun ya ce Kotu na da hurumin sauya hukuncin da ta yanke idan an yi ba daidai ba zaman sauraron karar
- Da farko, Kotu ta tunbuke Usman Baba daga matsayin sufetan yan sanda na ƙasa saboda shekarunsa sun kai ya yi ritaya
Anambra - Babbar Kotun tarayya mai zama a Awka, babban birnin jihar Anambra ta jingine hukuncin tsige Usman Baba daga matsayin sufetan 'yan sanda na ƙasa (IGP).
The Cable ta tattaro cewa yayin yanke hukunci ranar 19 ga watan Mayu, Alkalin Kotun, mai shari'a Fatun Riman, ya umarci Baba ya daina ayyana kansa a matsayin IGP.
Riman ya yanke hukuncin cewa zaman Baba a kan kujerar IGP bayan ya cika shekarun ritaya watau shekara 60, ya saɓa wa doka da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kotu ta ɗauki wannan matsaya ne a ƙara mai lamba FHC/AKW/CS/58/2023, wacce Okechukwu Nwafor, ya shigar gabanta, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
IGP ya kalubalanci wannan hukunci
Da yake kalubalantar hukuncin a gaban Kotun, IGP ta hannun lauyansa, ya shaida wa Alkalin cewa ba'a masa adalci ba a sauraron ƙarar saboda mai ƙara ya gaza kai masa takardar sammaci ta usuli.
Haka zalika Sufetan yan sanda ya yi ikirarin cewa wata babbar kotun tarayya mai zama a Abuja karkashin mai shari'a J.K. Omotosho ta yanke hukunci kan batun da ake tuhumarsa a kai a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/31/2023.
Kotu ta sauya hukuncin da ta yanke a baya
Da yake sake yanke hukunci ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2023, mai shari'a Riman, ya amince da bayana sufetan yan sandan Najeriya.
Alkalin ya yi bayanin cewa kundin tsarin mulki ya bai wa kowace Kotu, harda Kotun koli cikakken ikon sauya hukuncin da ta yanke a baya idan ta gamsu da hakan.
Ya ce:
"Bisa haka, hukuncin da wannan Kotun ta bayyana ranar 19 ga watan Mayu, 202l3, mun jingine shi saboda rashin sanar da wanda ake ƙara na biyu (IGP) game da shari'ar. Hukuncin wannan Kotun kenan."
Shugaba Tinubu Ya Gana da Ɗangote da Bello Matawalle
A wani rahoton na daban kun ji cewa shugaba Tinubu ya gana da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da Alhaji Dangote a fadarsa da ke Abuja.
Da yake hura da yan jarida, Matawalle ya kara da nuna yaƙinin cewa Tinubu zai kafa tarihin zama shugaban ƙasan da ba'a taɓa kamarsa ba a tarihi.
Asali: Legit.ng