Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Coci a Jihar Benuwai

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Coci a Jihar Benuwai

  • Yan bindigan da ake zaton masu garkuwa da mutane don neman fansa ne sun yi awon gaba da Malamin Coci a jihar Benuwai
  • Wani ganau mai suna Oche, ya shaida cewa maharan sun shiga garin da karfe 10:00 na daren ranar Alhamis, suka wuce kai tsaye zuwa harabar Coci
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin

Benue - Wasu miyagun 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da Malamin cocin Otukpo Diocese, Rabaran Anthony Adikwu.

Jaridar Punch ta tattaro cewa Malamin Cocin da maharan suka yi garkuwa da shi yana aiki a St. Margaret’s Parish da ke garin Ajegbe Awume, ƙaramar hukumar Ohimini a jihar Benuwai.

Taswirar Jihar Benuwai.
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Coci a Jihar Benuwai Hoto: punchng
Asali: UGC

Wani ganau da ya bayyana sunansa da Oche a takaice, ya shaida wa wakilin jaridar cewa wasu 'yan bindiga sun farmaki garin da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Aika Yan Ta'adda 42 Lahira, Sun Cafke Wasu 96 A Arewacin Najeriya

Ya ce daga zuwan yan ta'addan ba su tsaya wata-wata ba suka durfafi harabar Cocin, daga nan suka kwamushe Malamin suka tafi da shi maɓoyarsu da ba'a sani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ruwayar Tribune, Mista Oche ya ce:

"A daren jiya (Alhamis) da kusan karfe 10:00, wasu yan bindiga suka shiga garin Ajegbe Awume, karamar hukumar Ohimini ta jihar Benuwai. Kai tsaye suka zarce harabar Coci suka ɗauki Malamin da ke kula da majami'ar St. Margaret Parish.”

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka zuwa yanzu?

Yayin da aka tuntuɓe ta, Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar yan sanda reshen jihar Benuwai da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya, SP Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Anene ta ce:

"Rahoto ya iso gare mu da safiyar nan (ranar Jumu'a) kuma a halin yanzu muna kan aiki game da lamarin."

Kara karanta wannan

Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka

Jihar Benuwai na ɗaya daga cikin jihohin Arewa ta Tsakiya da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, waɗanda mafi akasari ake zaton makiyaya ne a sassan jihar.

Yan Boko Haram Kai Kazamin Hari, Sun Yi Wa Mutane 15 Yankan Rago

A wani labarin na daban kuma 'Yan ta'addan Boko Haram sun tarfa mutane a jihar Borno, sun yi wa mutane 15 yankan Rago.

Tsagerun yan ta'addan sun farmaki kauyen Kofa a karamar hukumar Jere ta jihar a daren Alhamis har zuwa wayewar garin Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262