Wayo Ya Kare: ’Yan Sanda Sun Kwamushe Bakin Haure 12 Daga Kasashen Ketare, Wadanda Saudiyya Ta Koro

Wayo Ya Kare: ’Yan Sanda Sun Kwamushe Bakin Haure 12 Daga Kasashen Ketare, Wadanda Saudiyya Ta Koro

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama bakin haure guda 12 da suka fito daga kasashen Mali da Niger
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a ofishinsa da ke Kano
  • Ya ce rundunar har ila yau, ta samu nasarar cafke wasu mutane 33 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta cafke bakin haure guda 12 daga kasashen Mali da Niger.

Rundunar ta kuma sanar da kama wasu bata gari guda 33 da suka addabi mutanen jihar da sata da sauran laifuka munana.

'Yan sanda sun cafke bakin haure 12 daga kasashen ketare a Kano
Yan Sandan Najeriya a Bakin Aiki. Hoto: Daily Post.
Asali: UGC

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a birnin Kano, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Aika Yan Ta'adda 42 Lahira, Sun Cafke Wasu 96 A Arewacin Najeriya

Ya ce bakin hauren sun fito daga kasashen ketare

Ya ce bakin hauren sun hada da 'yan kasar Mali guda bakwai da kuma 'yan Niger guda biyar da aka koro su daga Saudiyya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Akwai raunuka a jikin bakin hauren musamman yadda suka bata yatsunsu da abu mai kaifi don gudun kada a gane su yayin dangwala yatsa a na'ura don tantancewa.
"Sauran mutane 33 kuma an kama su ne da zargin aikata laifuka da suka hada da fashi da makami da sata da garkuwa da mutane da kuma mallakar bindigu."

Daga cikin abubuwan da aka samu a tare da su akwai wukake da wayoyi guda 46 da layin waya 21 da bindiga da kuma makullai na musamman.

An samu muggan kwayoyi a tare da matasan

Sauran sun hada da kwayoyin maye na diyazabam da kullin tabar wiwi 98 da ekzol 79 da sauransu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sai Na Ga Bayanku: Sabon Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Babban Tanadin Karar Da ’Yan Bindiga

Ya ce wadanda ake zargin za a tasa keyarsu zuwa kotu da zarar an kammala binciken da ya dace.

La'adar N200k: Yan Sandan Na Neman Wani Mutum Ruwa A Jallo Kan Mallakar Bindigu

A wani labarin, 'yan sanda a jihar Osun suna neman wani matashi mai suna Rotimi Orowole bisa zargin mallakar bindigu.

Matashin mai shekaru 31 ya tsere inda hukumar ta saka kyautar kudi ga duk wanda ya kawo shi.

Rundunar ta ce ta saka kudi har N200,000 ga duk wanda ya nemo bayanin yadda za a same shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.