Halin da Tsohon Gwamnan CBN Emefiele Ke Ciki Bayan Kwana 6 a Hannun DSS
- Har yanzu babu wani matakin doka da hukumar DSS ta ɗauka kwanaki 6 bayan kama dakataccen gwamnan CBN
- Godwin Emefiele ya shafe kusan mako ɗaya a tsare a hannun DSS tunda ya shiga hannu ranar Jumu'a da yamma
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Emefiele daga matsayin gwamnan CBN kana ya umarci a gudanar da bincike
FCT Abuja - Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya shafe kwanaki shida kenan a hannun hukumar yan sandan farin kaya (DSS).
The Nation ta rahoto cewa har zuwa yau DSS ta kama baki ta yi gum game da mataki na gaba da zata ɗauka kan Emefiele, zata gurfanar da shi a gaban Kotu ko a'a.
Jami'am DSS sun cafke Emefiele ranar Jumu'a da ta gabata da yamma jim kaɗan bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da shi daga matsayin gwamnan CBN.
Washe gari ranar Asabar, mai magana da yawun hukumar DSS ta ƙasa, Peter Afunanya, ya tabbatar da cewa Mista Emefiele na tsare a ofishinsu domin amsa wasu tambayoyi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa DSS ta cafke Emefiele?
Duk da bai faɗi makasudin tsare shi da, ana ganin hakan ba zai rasa alaƙa da zargin taimakawa ta'addanci da kuma karkatar da wasu kudaɗe a babban banki ba.
A watan Disamba, 2022, hukumar ta yi yunkurin samun umarnin Kotu domin damƙe Emefiele bisa zargin angiza wa yan ta'adda kudi, shiga harkokin damfara da sauransu.
Sai dai hukumar ba ta kai ga nasara ba domin ta gaza gabatar da kwararan hujjoji da zasu gamsar cewa Emefiele na da hannu a taimakawa ta'addanci da kuɗaɗe da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa.
Wane mataki DSS ta ɗauka kan Emefiele zuwa yau?
An yi tsammanin tun ranar Talata, DSS zata garzaya Kotu ta samo umarnin ci gaba da tsare dakataccen gwamnan CBN domin gudanar da bincike a tsanake.
Amma har zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton babu tabbacin ko hukumar ta samu umarni daga Kotu na ci gaba da rike Emefiele a hannunta.
Wata majiya ta ce:
"Wannan batu ne mai girma ba zan iya dogon zance a kai ba, amma hukumar DSS na kokarin ganin ta haɗa duk abinda take buƙata a wannan Kes ɗin. Ana kan bincike, ba zan cika surutu ba, mu jira mu gani."
Abbas Tajudeen, Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Nada Hadimai Biyu
A wani labarin kuma Kakakin majalisar wakilan tarayya, Honorabul Tajudeen Abbas, ya fara naɗa hadiman da zasu taimaka masa a majalisa ta 10.
Abbas Tajudeen, ya naɗa Musa Krishi a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan yaɗa labarai da midiya.
Asali: Legit.ng