La'adar N200k: Yan Sandan Najeriya Na Neman Wani Mutum Ruwa A Jallo Osun Kan Mallakar Bindigu

La'adar N200k: Yan Sandan Najeriya Na Neman Wani Mutum Ruwa A Jallo Osun Kan Mallakar Bindigu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta ayyana wani matashi mai suna Orowole Rotimi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo
  • Rundunar ta ce ana zargin Orowole Rotimi da mallakar muggan makamai da kuma ba wa rundunar bayanan karya
  • Jami'an 'yan sandan sun bayyana cewa duk wanda ya kawo bayanin yadda za a kama wanda ake zargin zai samu kyautar N200,000

Jihar Osun - Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta na neman wani matashi mai suna Orowole Rotimi ruwa a jallo bisa mallakar makamai.

Kakakin rundunar'yan sandan jihar, CSP Ayeni Benjamin ya ce ana zargin Orowole da mallakar makamai da kuma bai wa 'yan sanda bayanin karya.

Yan sanda sun bazama neman matashi da ya mallaki makamai
Jami'in Dan Sanda a Najeriya. Hoto: Daily Post.
Asali: UGC

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya gudu ba a san inda yake ba, kuma duk wanda aka gansu tare za a kamasu da laifi daya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Aika Yan Ta'adda 42 Lahira, Sun Cafke Wasu 96 A Arewacin Najeriya

Jami'an 'yan sandan na farautar matashin bisa zargin mallakar makamai

Tribune ta tattaro cewa Ayeni ya ce hukumarsu tun watan Yuni zuwa yau ta karbi korafe-korafe 52, 48 daga ciki ana bincikensu yayin da aka tura 8 zuwa kotu, wasu 8 din kuma suna jiran hukuncin karshe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Rundunar 'yan sandan shiyya ta Osogbo na farautar wani matashi da ake zargi da mallakar makamai da kuma sauran tuhume-tuhume akansa.
"Wanda ake zargin Orowole Rotimi ya tsere kuma ya ki zuwa don kare kansa a gaban jami'anmu.
"Muna sanar da jama'a cewa Orowole Rotimi dan Najeriya da ke Ile Ife wanda aka sanya hotonsa, muna nemanshi ruwa a jallo."

'Yan sanda sun saka kyautar kudi ga duk wanda ya kawo shi

Ya kara da cewa:

"Orowole Rotimi mai shekaru 31, mai hasken fata da fararen hakora kuma dan kabilar Yarbawa wani lokaci yana barin gemu, yana da sanko da kuma bakin gashi.

Kara karanta wannan

Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka

"Duk wanda ya bashi mafaka jami'an 'yan sanda za su hukuntasu da laifi iri daya, kuma duk wanda ya ba da bayanin inda yake zai samu kyautar kudi N200,000."

Tsagera Sun Sake Yin Garkuwa Da Mai Sarautar Gargajiya A Arewacin Najeriya

A wani labarin, mahara sun sace wani mai sarautar gargajiya a jihar Plateau da ke Arewa ta Takiyar Najeriya.

Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ne ya sanar da haka yayin bikin ranar Dimukradiya a jihar.

An sace Joshua Mutkut wanda shi ne Dagacin kauyen Mushere da ke karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.