An Maka Budurwa A Kotu Kan Sama Da Fadi Da Naira Miliyan 4 Da Ƙawarta Ta Ba Ta Ajiya A Abuja

An Maka Budurwa A Kotu Kan Sama Da Fadi Da Naira Miliyan 4 Da Ƙawarta Ta Ba Ta Ajiya A Abuja

  • An gurfanar da wata budurwa mai suna Oyetola Mofunrayo, mai shekaru 23, a Abuja, saboda tserewa da kuɗaɗen ƙawarta naira miliyan 4 a bikin zagayowar ranar haihuwarta
  • An tuhumi Mofunrayo da laifin cin amana, zamba, da kuma karkatar da kuɗaɗen da aka ɗanƙa a hannunta domin ajiya
  • Sai dai wacce ake tuhuma ta musanta zargin, inda ta haƙiƙance cewa babu wanda ya bata kuɗin domin ta ajiye

Abuja - A ranar Alhamis ɗin nan ne aka gurfanar da wata budurwa, Oyetola Mofunrayo, mai shekaru 23 a gaban wata kotu mai daraja ta ɗaya da ke Kado a Abuja, bisa laifin karkatar da kuɗaɗen ƙawarta ta naira miliyan 4 a ranar zagayowar ranar haihuwarta.

Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da Mofunrayo da ke a rukunin gidaje na Ochacho, Idu Abuja, da laifin zamba cikin aminci, cin amana, da karkatar da kuɗaɗe, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kishi Kumallon Mata: Yadda Matar Aure Ta Kona Budurwar Mijinta Da Ruwan Zafi a Fuska

Sai dai Mofunrayo ta musanta zargin aikata laifin da ake yi ma ta.

An gurfanar da matashiya kan laifin guduwa da kudi
'Yan sanda sun gurfanar da wata budurwa kan zargin guduwa da N4m. Hoto: City Lawyer Magazine
Asali: UGC

An bai wa budurwar kuɗaɗen a cikin jaka wajen bikin ranar haihuwa

Lauya mai gabatar da ƙara, Mista Stanley Nwafoaku, ya ce a ranar 20 ga watan Mayu da misalin karfe 4:30 na yamma, ya karɓi rubutaccen koke da Leo, lauyan mai shigar da ƙara Misis Jennifer Ephraim kan Oyetola Mofunrayo ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwafoaku ya ce a ranar 24 ga watan Agusta, mai shigar da karar ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta a Moscos Lounge da ke Abuja, inda aka ba ta kyautar kuɗi naira miliyan huɗu.

Ya ce wacce ta shigar da ƙarar ta bai wa hadimarta Mary John, kuɗaɗen da ke cikin wata jaka, sannan ta umarce ta da ta bai wa wacce ake ƙara domin ta ajiye mata.

‘Yan sandan sun bayyana cewa, washegari Misis Ephraim ta kira Mofunrayo domin ta kawo mata kuɗin, amma sai ta ƙeƙashe ƙasa ta ce ba a bata wasu kuɗaɗe a cikin jaka ba.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Yi Ram Da Matasa 5 Da Suka Lakadawa Mata Da Mijinta Duka A Abuja

Jami'an sun ce a yayin da suke gudanar da bincike, wacce ake ƙara ta bayyana cewa wayar hadimar mai ƙarar na cikin jakar da aka sanya kuɗin a ciki.

Nwafoaku ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 312, 322 da 309 na dokar manyan laifuka.

An bayar da belin budurwar da ake ƙara kan N2m

Lauyar da ke kare wacce ake ƙara, Charity Nwosu ta gabatar da bukatar ba da belinta baka, inda ta ambaci sashe na 36 na kundin tsarin mulkin 1999, da sashe na 158 na dokar shari’a ta laifuka, na 2015.

Lauyar ta bayar da tabbacin cewa wacce ake karar ba za ta tsallake beli ba, idan aka ba ta.

Nwafoaku, bai ƙi amincewa da bukatar ba da belin da lauyan da ke kare wacce ake ƙara ta yi ba.

Alƙalin kotun, Malam Muhammed Wakili, ya bayar da belin wacce ake tuhuma a kan kuɗi naira miliyan biyu da kuma mutum ɗaya da zai tsaya mata.

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

Wakili ya ba da umarnin cewa wanda zai tsaya mata dole ne ya kawo kwafi na BVN, Fasfo da kuma ingantaccen katin shaida, wanda magatakardan kotun zai tabbatar da sahihancinsu.

Alƙalin kotun ya ɗage shari'ar zuwa ranar 10 ga watan Yuli domin sauraren karar.

Gini ya rushe masu kwasar ganima a Kano

A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa wani gini ya danne masu kwasar ƙarahunan gine-ginen da aka rushe da sunan ganima a Kano.

Ginin Daula Otal, wanda gwamnatin Abba Gida Gida ta fara rusawa, ya faɗa kan wasu da suka zo ɗinar ƙarahuna da sunan ganima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng